Gidauniyar Daily Trust tare da hadin guiwar Gidauniyar McArthur ta shirya wa ’yan jarida bitar kwana uku kan yadda ake binciken kwakwaf a hedikwatar Kamfanin Media Trust, mawallafan jaridar Aminiya da Daily trust a Abuja.
Yayin bude taron bitar, Mukaddashin Shugaban Kamafanin Media Trust, Malam Nura Daura, ya bai wa mahalarta shawarar su kara dagewa a bangaren binciken kwakwaf domin su bambanta da sauran gama garin ’yan jarida masu yin rahotannin yau da kullum kadai.
- Jami’an EFCC sun yi wa gidan Okorocha kawanya
- NAJERIYA A YAU: Hukuma Ce Kadai Za Ta Iya Hana Bara —Malamin Addini
Nura Daura ya kara da cewa, “Kowa zai iya shiga kafofin sada zumunta ya wallafa abinda ya ga dama, amma idan aka yi maganar binciken kwakwaf, wannna wani abu ne na daban.
“Yana bukatar lokaci da kudi da kuma kwarewa, shi ya sa muka mayar da hankali wurin bayar da horo na musamman kan irin wannan aikin na binciken kwakwaf”.
Shugaban talabijin din Aminiya Ibrahim Shehu a yayin bikin ya baiwa mahalarta taron shawarar su jajirce wurin binciko da yada labaran gaskiya ta hanyar cire tsoro da binciken kwakwaf.
Ya ce, “Dan jarida mai binciken kwakwaf yakan bayyana abin da wadansu ke boyewa ne, don haka dole ne ya zama yana da hujjoji masu kwari domin tabbatar da abin da ya binciko.”
Daraktan Gidauniyar Daily Trust, Theophilus Abbah, a yayin nasa jawabin, ya ce an shirya taron bitar ne domin inganta aikin jarida da kara karfafa bangaren binciken kwakwaf ta hanyar amfani da sahihan bidiyo da kuma sauti.
Bitar ta hada ’yan jarida daga gidajen talabijin da rediyo da jaridu da kuma kafafen yada labarai na zamani daga ciki da wajen Najeriya.