Gidauniyar Daily Trust ta gudanar da taron kara wa juna sani na kwana uku ga ’yan jaridu a kan yadda ake amfani da na’urorin sadarwa na zamani.
Da yake jawabin bude taron, Shugaban Gidauniyar, Alhaji Bilya Bala ya ce dole ne ’yan jaridu su nemi masaniyar aiki a zamanance da kuma yadda za su sarrafa na’urorin zamani.
- Batanci ga Annabi: An kashe matashi an kona gawarsa a Bauchi
- Aguero zai yi bankwana da Manchester City a karshen kaka
Taron wanda ya gudana a dakin taron Gidauniyar da ke Utako a Abuja, ya samu halartar ’yan jarida 24 daga kafafen yada labarai daban-daban.
Shugaban Gidauniyar wanda ya samu wakilcin daya daga cikin wakilan gidauniyar, Alhaji Umar Abdullahi, ya ce wajibi ne ’yan jarida su samu ilimin sabbin na’urorin aiki wadanda zamani ke tafiya da su.
A cewarsa, a wannan lokaci na sauyin zamani da ake amfani da fasahar zamani wajen yada labarai, dole ne duk dan Jarida ya san yadda zai aika labarai ta kafofin labarai daban-daban.
Ya ci gaba da cewa dole ne ’yan jarida su san yadda za su rika amfani da shafukan labarai daban-daban na zamani don su tafi dai dai da zamani.
Alhaji Bilya Bala ya karfafa wa mahalarta taron gwiwar kar su yi kasa a gwiwa, su jajirce a fagen yada labarai, babu gudu, babu ja da baya.
A nasa tsokacin, Daraktan Gidauniyar, Dokta Theophilus Abbah, ya ce ana horar da su ne don cimma kalubalen zamani a fannin fasahar labarai.
Ya ce taron horarwan da Daily Trust Foundation ta shirya Gidauniyar Mac-Arthur ce ta dauki nauyin gudanarwa.