Dandalin sada zumunta na WhatsaApp ya ce ya kawo wasu sabbin tsare-tsare guda uku da za su karfafa adana bayanan sirrin abokanan huldarsu da ciki har da hana daukar hoton tattaunawa ko yin ‘screenshot’ a turance.
Kamfani Meta, wanda ya mallaki dandalin na WhatsApp da ma wasu ne ya bayyana hakan, ta bakin mamallakinsa, Mark Zuckerberg.
- Serena Williams za ta yi ritaya daga buga wasan tennis
- An kara kudin wutar lantarki da kaso 75 a Sri Lanka
Matakin, a cewatsa, zai kara ba da kariya ga sirrin masu amfani da manhajar ta whatsaApp.
Tsare-tsaren dai sun hada da ficewa daga dandali ba tare da nusar da sauran mambobi ba, sai masu tafiyar da shi, da a baya babu shi.
Sai kuma zabin iyakance wadanda za su iya ganin loakcin da kake amfani da manhajar, da shi ma a baya sai dai ka rufe kowa da kowa, ko kuma ka bude kowa.
Sabon tsarin ya kuma tanadi damar ficewa daga dandali wato group ba tare da kowa ya sani ba.
“Muna farin cikin sanar da abokan huldar mu cewa za mu ci gaba da iyakar kokarinmu domin ganin mun samar da tsarin da za ku gamsu da mu na kare bayananku na sirri,” inji sanarwar.
Idan ba a manta ba dai a watan Mayun 2022 ne kamfanin ya fitar da wani sabon tsarin na ba wa shugabannin dandali damar goge sako ga kowa da kowa.