✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gidan surukai

Wani saurayi ne ya je gidan surukansa, aka kawo masa cincin da lemun kwalba. Aka yi ta fama da shi ya ci ya ce a’a.…

Wani saurayi ne ya je gidan surukansa, aka kawo masa cincin da lemun kwalba. Aka yi ta fama da shi ya ci ya ce a’a. Sai surakansa suka ce bari su ba shi wuri, kila yana jin kunya ne, ita ma budurwarsa ta ce bari ta ba shi wuri. Aka bar shi a falo shi kadai, sai goganka ya cire hularsa ya juye rabin cincin cikin hula, ya mayar a kansa. Aka zo aka ce: “Kai dai ka ki cin komai?” Sai ya ce: “Ai wallahi na koshi ne.” Ya ce zai tafi, ya fito tsakar gida zai yi sallama da surukai sai igiyar shanya ta ja hularsa baya; sai ga cincin sharrrrrrrr a kasa. Sai gogan naka ya ce: “Ah, ah, yau ruwan cincin ake yi kuma?”

Daga Iliyas Idris Fahad Suleja, 07086228845