✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gidan Rediyon Katsina zai ci gaba da ba kungiyoyi goyon baya – Alhaji Nasiru

Gidan Rediyon Jihar Katsina ya yi alkawarin ci gaba da tallafa wa kungiyoyin da ke fadin jihar ta hanyar yada ayyukan da suke yi.Sabon Manajan…

Gidan Rediyon Jihar Katsina ya yi alkawarin ci gaba da tallafa wa kungiyoyin da ke fadin jihar ta hanyar yada ayyukan da suke yi.
Sabon Manajan Gidan Rediyon, Alhaji Nasiru Isma’ila ne ya bayyana haka a kwanakin baya,  lokacin da wakilan kungiyar Muryar Talakka reshen Jihar Katsina suka kai masa ziyarar taya murna a kan sabon mukaminsa. Manajan ya tabbatar wa wakilan cewa, “hukumar gidan rediyon na alfari da irin ayyukan da kungiya suke aiwatarwa domin kawo ci gaba a tsakanin al’umma.
Kune kashin bayan cigaba ba wai ta fuskar kafofin yada labarai ba kawai hatta da zamantakewa a tsakanin al’umma ta irin yadda kuke sadaukar da rayukarku don ganin cewa al’umma sun ci gaba”.
Daga nan manajan ya yaba da ayyukan kungiyar wadda ke “kokarin fadakar da jama’a ko ilmantar da su a kan abubuwa da dama ba sai wadanda suka jibanci na gwamnati ba,” inji shi.