✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

George Bush na yi wa kanensa kamfen

A ranar Talatar da ta gabata ne tsohon Shugaban Amurka, George W Bush, ya fara taya kanensa Jeb Bush yakin neman zabe da zummar taimaka…

A ranar Talatar da ta gabata ne tsohon Shugaban Amurka, George W Bush, ya fara taya kanensa Jeb Bush yakin neman zabe da zummar taimaka masa wajen samun tikitin yi wa jam’iyyar Republican takara a zaben bana.
Jeb Bush dai yana sahun baya a cikin jerin mutanen da ke son yin takarar Shugabancin Amurka na jam’iyyar ta Republican, inda Donald Trump da Ted Cruz suka yi masa zarra, kamar yadda BBC ya bayyana.
George W Bush ya gana da tsofaffin sojoji, sannan ya je wajen yakin neman zabe a Jihar South Carolina ranar Litinin, gabanin zaben fitar da dan takarar da za a yi ranar Asabar mai zuwa .
George W Bush ya sha suka a wajen Mista Trump, wanda ya rika aibata ire-iren ayyukan da ya yi a lokacin da yake shugabancin kasar daga shekarar 2001 zuwa 2009.
Jeb Bush, wanda tsohon gwamnan Jihar Florida ne, ya kashe kudin da dama wajen yakin neman zabe amma har yanzu bai yi wani tasiri ba.