Gwamnan Jihar, Mai Mala Buni ya ziyarci Jihar Kano domin ta’aziyyar rasuwar Mai Babban Daki, mahaifiyar Sarkin Kano, Hajiya Maryam Ado Bayero.
Mai Mala Buni tare da Shugaban Majalisar Dattawa, Ahmad Lawan, sun bar Abuja ne a safiyar Alhamis domin ziyarar ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar ta Sarkin Kano, wadda ta rasu a ranar Asabar.
- Yadda Boko Haram ta raba kyautar kudade a Geidam
- Rashin fada wa gwamnati gaskiya ne ya jefa Najeriya cikin rikici — Osinbajo
Bayan yi wa Sarki Aminu Ado Bayero da kaninsa, Sarkinin Bichi, Nasiru Ado Bayero ta’aziyyar rasuwar mahaifiyar tasu, wadda Allah Ya yi wa cikawa a kasar Masar, Buni da Lawan sun zarce zuwa Sakkwato.
A Sakkwaton, sun yi wa Magajin Garin Sakkwato, Alhaji Hassan Danbaba ta’aziyyar rasuwar mahafiyarsa, Hajiya Aishatu Ahamdu Bello, wadda ta rasu a ranar Juma’a.
Marigayi Hajiya Aishatu, ita ce ’yar marigayi Sardauna Sakkwato, Alhaji Ahmadu Bello.
Sanarwar da mai magana da yawun Shugaban Majalisar Dattawa, Ola Awoniyi ya fitar ta ce a ranar Alhamis din ake sa ran Buni da Lawan za su sake dawowa Abuja.