✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gbajabiamila ya gana da Osinbajo

Shugaban Majalisar Wakilai, Mista Femi Gbajabiamila ya gana da Mataimakin Shugaban Kasa a ranar Ltinin da ta gabata a fadar Shugaban Kasa da ke Abuja.…

Shugaban Majalisar Wakilai, Mista Femi Gbajabiamila ya gana da Mataimakin Shugaban Kasa a ranar Ltinin da ta gabata a fadar Shugaban Kasa da ke Abuja. Mista Gbajabiamila wanda aka zaba a ranar Talatar da ta gabata ya gana da Mataimakin Shugaban Kasa na tawon awa daya. Da yake yi wa manema labarai karin bayani game da ganawar, ya ce ya je fadar ce domin su tattauna wasu muhimman batutuwa da suka shafi kasa.

“Ziyarar ta aiki ce, kuma kun san duk wata tattaunawa da za mu yi da Mataimakin Shugaban Kasa tana da muhimmanci. Mun tattauna ne game da tattalin arziki da yadda za mu ciyar da kasar gaba, muna kokarin fiddo da wasu hanyoyi na warware matsalolin da suka addabi kasarmu a yanzu. Wadannan su ne abubuwan da muka tatttauna, ba wani abu na kashin kaina ba, amma in kun so za ku iya cewa akwai ma wasu dalilan na kaina to sai dai dalilan aikin su suka fi karfi. Akwai kuma batun yadda Bangaren Zartarwa da na Majalisa za su hada kai domin mu saita Najeriya saboda amfanin ’yan Najeriya,” inji shi.

Ya yi alkawarin fasalta majalisar domin kowane bangare na kasa a dama da shi. Ya ce “Ku ci gaba da saurarenmu, kamar yadda na fada a jawabina na farko a kan wannan mukami, za mu yi abin da ya sha bamban da wanda aka gani a baya, za mu kawo sauye-sauye da za su kawo nasara a wannan majalisa karo na 9.”

“Kamar yadda na fada za mu sake wa majalisa fasali ta yadda za ta shafi kowane bangare, kuma ta amfani kasa,” inji shi.

Don cimma wannan burin “Muna bukatar hadin kan Bangaren Zartarwa da ku ’yan jarida da kuma sauran jama’ar kasa,” inji shi.

Ya ce “Dukkan sauran nade-nade na kwamitocin da za a yi a majalisa za a yi su a makonni masu zuwa. Kuma za mu hada da bangaren ’yan adawa, ba zan yi azarbabi ba, amma ina mai tabbatar muku cewa za mu yi komai da su.”