Mataimakin Gwamnan Jihar Kano, Nasiru Yusif Gawuna ya lashe zaben fidda-gwanin Gwamna da jam’iyyar APC ta gudanar a Jihar.
An fitar da sakamakon yadda jadawalin zaben fidda gwanin ya gudana a ranar Juma’a, inda Gawuna ya samu kuri’a 2,289, yayin da Sha’aban Ibrahim Sharada, dan Majalisar Wakilai mai wakiltar mazabar Birnin Kano da Kewaye ya samu kuri’a 30.
- Ya kamata a yi dokar da za ta hana raba wa daliget kudi —Jonathan
- Gwamnan Anambra ya ba mijin da aka kashe wa mata da ’ya’ya N500,000
Shugaban kwamitin zaben, Tijjani Yahaya ne, ya sanar da Gawuna matsayin wanda ya yi nasara a zaben.
An gudanar da zaben fidda-gwanin a ranar Alhamis a filin wasa na Sani Abacha da ke birnin Kano.
Tun farko, Sha’aban Sharada ya yi korafin cewar tsagin Gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje na shirin yin magudi don ganin dan takarar gwamnan, Gawuna ya yi nasara.
Tun kafin shiga zaben fidda gwanin, Ganduje ya fitar da Gawuna da tsohon Kwamishinan Kananan Hukumomin Jihar, Murtala Sule Garo a matsayin ‘yan takarar APC a Kano.
Lamarin dai bai wa wasu da dama dadi ba, har ta kai ga ficewar irin su Abdulmumin Jibrin Kofa da Kawu Sumaila, zuwa jam’iyyar NNPP.