Ga ci gaba da tattaunawa tsakanin Habu Mai Kunya da Dauda kulu:
Habu Mai Kunya: Wane Shugaban kasa kake nufi? Shugaban kasar da ya yi wancakali da dukkan tanade-tanaden tsarin mulki, ya watsar da ka’idar dimokuradiyya, a yayin da yake fafutukar ganin cewa ya sake darewa kan mulki a karo na biyu? Kuma ka sani, Sanusi Lamido Sanusi ba shi ne jami’in gwamnati na farko da aka taba wulakantawa ba kuma ba shi ne zai zama na karshe ba. Idan ba mu mance ba, ai an yi wa Mai Shari’a Ayo Salami irin wannan wulakanci. Kuma shi ne yanzu za ka ce wai Shugaban kasa yana kishin gwamnati? Ba ni dai za ka gaya wa haka ba, sai dai ka tsara kaji, domin zabbi tashi suke.
Dauda kulu: Ni dai na san babu abin da ke damun ku sai bakin ciki kuma ko kuna so, ko ba ku so Jonathan sai ya zarce da mulki a 2015.
Habu Mai Kunya: Allah bai kyale Najeriya ba, ba zai bari ta ci gaba da wulakanta a hannun wannan gwamnati marar kan gado ba. Haba, ina za mu so a ce mun ci gaba da zama a tare da gwamnatin da ke yin kwangilar Naira goma a kan Naira dubu daya? Sannan kuma a ce za mu ci gaba da tafa mata, kamar dai satar dukiyar jama’a ba laifi ba ne? Ya zama wajibi mu kori Jonathan da mukarrabansa a 2015. Abin da zai faru ke nan, kai dai ci gaba da kallo, ranar za ta zo. Mutane irinku za su kare ne a gidan kurkuku saboda muggan laifukan da kuka aikata.
Dauda kulu: Bakinka ya sari danyen kashi! Babu wani abu mai kama da haka da zai faru. Duk tarin jam’iyyun nan da suka yi hadin gwiwa, ba za su kama kafar Jonathan ba. Kuma idan ma zan tambaye ka, shin wane ne kake jin zai maye gurbinsa – kana nufin wadannan munafukan masu yawan taratsi?
Habu Mai Kunya: Saurara ka ji, kada ka ce za ka yi riga malam masallaci. Mu ba mu kasance masu karya doka kamar jam’iyyarku ba. Ka duba fa ka gani, har Jonathan ya fara kamfe. Idan ka duba, duk shafin da ka buda a intanet, za ka ga tallar Jonathan, ana gayyatar mutane wai su zama ’yan Jonathan. Shi kansa Shugaban kasar yana ta yawo daga fadar wannan sarki zuwa fadar wancan saraki, yana neman goyon bayansu. Haka kuma duk inda ka duba a Abuja, za ka ga fostar Jonathan an lillika. Duk da haka amma Hukumar Zabe ba ta ce kala ba, alhali ana karya dokar zabe.
Dauda kulu: Ji abin da kake fada, Jonathan ai ba shi ne ke sanya wadannan tallace-tallace ba. Masu kaunarsa ne da sauran masu kaunar Najeriya ke yin wadannan abubuwa. Kuma wannan ai ba riga malam masallaci ba ne. Ku dai kuna nuna kishi ne kawai ga Jonathan domin har yanzu kun kasa samun dan takarar shugabancin kasa kamarsa. Yana da farin jini da karfi a Kudancin Najeriya, ga shi kuma kashi uku cikin hudu na ’yan Arewa suna son shi. To, me ya rage?
Habu Mai Kunya: Abin da ya rage shi ne, ku farka daga mafarkin da kuke yi. Jonathan yana da babbar matsala a Jihar Ribas, jihar da ta fi kowace girma a Kudancin Kudun kasar nan. Ya kasance abin kyama a dukkan sassan yankunan Arewa, a yayin da al’ummar Kudu Maso Yamma suka dauke shi kamar dan kama – abin dariya. kokarin da ya yi na raba kan al’ummar Ibo da kuma yadda yake kokarin yin amfani da addini wajen raba kan al’umma ba zai yi tasiri ba. Wannan munafuncin zai zama dodo ya halaka nufinsa.
Dauda kulu: Ni dai ina ganin ya dace ka je likita ya duba lafiyar kanka, domin kuwa ba ka da hankali. Jonathan shi ne Shugaban kasa mafi inganci da muka taba samu tun da mulkin dimokuradiyya ya dawo. Mulkinsa ya kyautata wa dukkan al’ummar Najeriya. Ban ce ya samu nasara dari bisa dari ba amma dai shi ya fi kowane Shugaban kasa nasara a kasar nan ya zuwa yanzu. Wawaye irinku ne kadai da jam’iyyun adawa ba su ganin nasarar da Jonathan ya samu.
Habu Mai Kunya: Babu mai zage-zage sai shashasha, wanda ke tare da barayin dukiyar al’umma. Ka tsaya mu tattauna kai tsaye, ba tare da kaucewa daga maudu’in ba. Ni na san cewa Sanusi Lamido zai fito a matsayin wankakke daga kashin kajin da kuke shafa masa. Ku kwace masa fasfot, ku gurfanar da shi gaban kotu, ku tura karnukan EFCC gare shi, wannan duk ba za ta huda ciki da gaskiya ba – ko za ka iya tuna cewa Obasanjo ya tsallako daga ramin mutuwa ne ya zo ya zama Shugaban kasa? Shi Jonathan ya biyo ’yar zagaye ne, don haka zai koma ya biyo hanyar da za ta nutsar da shi zuwa ramin…
Dauda kulu: Wannan tunanin banza ne! Sanya Sanusi a wannan mukamin ai kuskure ne, yanzu Jonathan ya gyara wannan kuskuren.
Habu Mai Kunya: A’a, Jonathan a kan mulki shi ne kuskure tun daga ranar farko. Tun da farko, kamata ya yi kawai a ce mun saya masa takalmi ya koyi tafiya, maimakon mu dora masa nauyin al’ummar Najeriya da suka dade suna shan wahala. Ga shi yanzu mun bari ya samu takalma sama da kafa dubu daya, shi ya sanya yake kara lalacewa a kullum.
Dauda kulu: Allah wadaran ka!
Habu Mai Kunya: Kai ma haka!
Gatarin zalunci a kan Sanusi Lamido Sanusi (2)
Ga ci gaba da tattaunawa tsakanin Habu Mai Kunya da Dauda kulu:Habu Mai Kunya: Wane Shugaban kasa kake nufi? Shugaban kasar da ya yi wancakali…