Hukumar Kidaya ta Kasa (NPC) ta karyata masu cewa ta shirya kidaya Musulmi ne da sunan akidun da suke bi maimakon a matsayin Musulmi baki daya a kidayar da za ta gudanar bana.
Kwamishinan hukumar a Jihar Gombe, Abubakar Mohammad Danburam, ya karyata batun da ake yadawa cewa a fom din cikewar akwai batun Kiristanci da Sunna da Tijjaniya da Shi’a amma ba a ambaci ambaci addinin Islama ba kai-tsaye.
Zargin da ke yawo a kafofin sada zumunta na cewa an shirya hakan ne domin yi wa Musulmin Najeriya manakisa a kidayar da za a gudanar da nufin rage alkaluman yawan Musulmai.
Masu yada zargin na cewa a daukar bayanan kidayar jama’a da hukumar ta tsara ta tambayi mutum addininsa, kuma a cikin zabin addinan aka sanya akwai addinin Kirista, amma maimakon a sanya Musulunci sai aka sanya akidu kamar Sunni da Shi’a da Tijjaniya da sauransu.
Ana zargin ke cewa ganin cewa Musulmi ne mafi yawan al’ummar Najeriya, aka shirya wannan makarkashiyar domin a nuna cewa mabiyan wanu addini sun fi su yawa.
Amma a hirarsa da wakilinmu, kwamishinan hukumar a Jihar Gombe, Abubakar Mohammad Danburam, ya karyata batun da cewa wasu masu adawa da kidayar ne suke yada ji-ta-ji-tar da nufin jawo wa shirin kyama.
A cewarsa, nan gaba kadan hukumar za ta fitar da sanarwar da za ta karyata zargin.
Kidayar 2023 za ta fi na baya inganci
Ya bayyana cewa kidayar ta wannan shekara za ta fi na shekarun baya saboda za a yi amfani da fasahar zamani wajen gudanar da aikin.
Danburam ya bayyana hakan ne a lokacin da Mataimakin Gwamnan Gombe, Manasseh Daniel Jatau, ya kaddamar da wani Kwamitin Mutum 16 da za su jagoranci aikin kidayar a jihar.
Ya kara da cewa hukumar ta shirya tsaf don gudanar da aikin kuma a baya ta yi kidaya na gwaji do ta gwada naurorinta kuma komai ya tafi daidai.
A cewar Danburam, kusan mutum dubu 40 ne suka nemi aikin kidayar a Jihar Gombe inda dubu 9 daga ciki suka yi nasara.
A jawabinsa na kaddamar da kwamitin, mataimakin gwamnan jihar, Manasseh Daniel Jatau, cewa ya yi makasudin kidaya shi ne don samun cikakken bayanin al’umma wanda zai taimaka wajen inganta tattalin arzikin al’umma.
Ya ce aikin kidaya ta hanyar amfani da nau’ra zai rage yawan matsalolin da suka rike wa hukumar wuya tare da kawar da bambancin siyasa da addini da son zuciya.
“Amma dai mu sani ita naurar mutum ke sarrafa ta, a wani lokaci za a iya samun matsala, amma zai zo da sauki,” in ji shi.
Daga nan sai ya bukaci ’yan kwamitin da su sadaukar da kansu wajen yin aikin yadda ya dace domin ganin an gudanar da kidayar cikin nasara.