✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Gaskiya ta fi kwabo’

Barka da warhaka Manyan Gobe Assalamu alaikum Manyan Gobe yaya hutu? Da fatan ana lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘gaskiya tafi kwabo’. Labarin…

Barka da warhaka Manyan Gobe

Assalamu alaikum Manyan Gobe yaya hutu? Da fatan ana lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘gaskiya tafi kwabo’. Labarin na kunshe da yadda gaskiya ta karbi wata mata Binta da mahaifinta Musa . A sha karatu lafiya.
Taku; Gwaggo Amina Abdullahi

‘Gaskiya ta fi kwabo’

Malam Bello mutum ne wanda aka fi saninsa da son kai. Allah Ya azurta shi da kudi. Rannan sai ya batar da sisin gwal guda 30. Abin ya yi masa ciwo. Sai ya je wajen abokinsa Malam Musa. Ya bayyana masa abin da ke damunsa. Sai Malam Musa ya ce Allah Yasa ya samu.
Washe gari, sai ga ‘yar Malam Musa ta dawo daga sayan itace. Sai ta ce da mahaifinta akan tayi tsintuwar sisinan gwal guda 30. Nan take Malam Musa ya aika a kira masa Malam Bello.
Yana isa sai Malam Musa ya danka masa sisina 30 akan cewa ’yarsa ta samo masa. A maimakon Malam Bello ya yi godiya, kuma ya yi wa abokinsa kyauta game da hakan. Don mako sai ya ce ai sisina 40 ne suka bata ba 30 ba. Malam Musa kuma ya ce ba zai biya ba.
Sai kara ta isa wajen alkali. Aka zayyana masa yadda komai ya faru. Alkali ya ce da Malam Bello sisinan gwal 30 da ‘yar Malam Musa ta samo ba nasa ba ne, domin nasa guda 40 ne. saboda haka, sai ya je shi idan an samo sisina 40 za a yi masa magana.
Jin haka, sai Malam Bello ya ce ai karya yake dama sisina 30 ne nasa ya bata. Alkali ya ki ya ji abin da Malam Bello ya fada. A hakan ya yi asarar sisina 30.