✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

‘Gaskiya Ta Fi Kwabo’

Assalamu alaikum Manyan Gobe yaya hutu? Da fatan ana lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Gaskiya Ta Fi Kwabo’. Labarin na qunshe ne da…

Assalamu alaikum Manyan Gobe yaya hutu? Da fatan ana lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Gaskiya Ta Fi Kwabo’. Labarin na qunshe ne da yadda gaskiya ta janyo wa Binta ’yar Malam Musa arziki a dare xaya.  A sha karatu lafiya.

Taku; Amina Abdullahi

Malam Bello mutum ne da aka shaide shi da son kai. Allah Ya azurta shi da kudi. Ran nan sai ya zubar da sisin gwal 30 ya yi nema amma bai gani ba.. Abin ya yi masa ciwo. Sai ya je wajen abokinsa Malam Musa ya bayyana masa abin da ke damunsa. Sai Malam Musa ya ce zai taya shi nema har Allah Ya sa a dace.

Washegari, sai ga ’yar Malam Musa mai suna Binta ta dawo daga sayen itace. Sai ta nuna wa mahaifinta Malam Musa tsintuwar da ta yi na sisin gwal 30.  Nan take Malam Musa ya aika aka kira masa abokinsa Malam Bello kuma ya shaida masa abin da ke faruwa na gano sisin gwal 30 dinsa da suka bace cewa ’yarsa Binta ce ta gano su. Da Malam Bello ya ga haka, sai ya kekasa kasa ya ce ai sisin gwal 40 ne nasa suka bata ba 30 ba don haka tilas sai Malam Musa ya biya shi sauran sisin gwal 10.

Daga nan magana sai wajen alkali.  Da alkali ya saurari dukkan bangarorin biyu sai ya gane akwai walakin, wai goro a miya.  Nan take sai ya zartar da hukuncin mayar wa Malam Musa sisin gwal 30 da ’yarsa ta tsinto kuma ya nuna cewa ba na Malam Bello ba ne, tun da nasa gwal 40 ne suka bace don haka sisin gwal 30 ba nasa ba ne.

Jin haka sai Malam Bello ya yi farat ya ce da ma wasa yake yi, sisin gwal 30 nasa ne amma alkalin ya ki amincewa ya nuna ai kotu ta riga ta zartar da hukunci, don haka tilas Malam Bello ya amince.

Daga nan ne Malam Bello ya shiga yin nadama, don ya tashi bashi da tsuntsu kuma ba shi da tarko, garin nema kiba sai ya samo rama.

Manyan Gobe, darasin wannan labari shi ne illar yin karya, don haka Gaskiya Ta Fi Kwabo.