✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar zakarun kulob na Turai: A ranar Laraba Arsenal za ta san matsayinta

A cigaba da fafafawa a gasar zakarun kulob-kulob na Turai (UEFA Champions League) a ranar Laraba 4 ga watan Nuwamban 2015 ne, kulob din Arsenal…

A cigaba da fafafawa a gasar zakarun kulob-kulob na Turai (UEFA Champions League) a ranar Laraba 4 ga watan Nuwamban 2015 ne, kulob din Arsenal zai san matsayinsa,  bayan ya fafata da kulob din FC Bayern Munich na Jamus a wasa karo na hudu.  Idan za a tuna Arsenal ta lallasa Bayern a gida ne kimanin makwanni biyu da suka wuce da ci 2-0.  Sannan Arsenal tana fafatawa ne a rukunin da ya kunshi kulob din Bayern Munich da  Olympiakos da kuma Dinamo Zagreb.
Duk da yake Arsenal ce ta doke na Munich da 2-0 a wasan da suka yi kimanin makwanni biyu da suka wuce amma kawo yanzu kulob din ne na karshe a rukunin da maki uku.
Kenan idan Bayern Munich ta doke Arsenal a gidanta sannan Olympiakos kuma ta doke Dinamo Zagreb zai kasance Arsenal ta shiga cikin tsaka mai zuwa. Kawo yanzu Munich ce kan gaba a rukunin da maki 6 sai Olympiakos mai maki 6 sai Dinamo Zagreb mai maki 3 yayin da ita ma Arsenal ke da maki 3. Don haka idan Munich ta doke Arsenal za ta hada maki 9 kenan yayin da in Olympiakos ta samu nasara akan Dinamo Zagreb ita ma za ta hada maki 9 kenan inda zai kasance Arsenal da Dinamo suna da maki uku-uku kenan kuma saura wasanni bibbiyu a zagayen farko na gasar.
kungiyoyin kwallon da suka kasance na daya da na biyu a kowane rukuni ne ke hayewa zagaye na biyu a gasar.