Wakili a Majalisar Manyan Malaman Saudiyya, Sheikh Abdullah Al-Manea, ya ce gasar kalubale a shafukan sada zumunta musamman fitaccen shafin nan na TikTok wani nau’i ne na caca.
Haka kuma Sheikh Al-Manea ya ce gasar wani salo ne na cin dukiyar mutane ta hanyar karya wanda addinin Musulunci ya haramta.
Jaridar Okaz/Saudi Gazette ta ruwaito Shehin Malamin yana cewa: “Wannan nau’in wasa ko aiki ba halattacce ba ne ta kowace hanya inda mutum biyu na jinsi guda ko jinsuna za su yi wasa.”
Sheikh Almanea wanda wakili ne a Cibiyar Fikhun Musulunci ta Duniya (International Islamic Fikh Academy), ya shaida wa jaridar Okaz/Saudi Gazette, cewa hakan caca ce ta yiwuwar biyan kudi ko samun ganima, kudin da aka sa shi ne na gasar,kuma akwai yiwuwar daya ne zai ci kudin.”
Fatawar ta malamin tana zuwa ne a daidai da gasar kalubale a manhajar TikTok take tashe a shafukan sadarwar zamani.
Wannan manhaja ta zama wata kafa ta aika kananan faya-fayen bidiyo na gasannin rawa da ban-dariya da takala da nuna wayo da bayar da tsoro da nishadantarwa na tsawon dakika 15 zuwa minti 10.
Gasar kalubale ta TikTok wani kamfe ne ko salon a gayyatar mutane su kirkiri bidiyonsu kan wani kalubale kamar nuna hazaka ko gwaninta kan wani abu