✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar share fage: Najeriya za ta kece raini da Kamaru ranar Litinin

A kokarin hayewa gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a shekara mai zuwa (2018) a ranar Litinin mai zuwa 28 ga…

A kokarin hayewa gasar cin kofin duniya da za a yi a Rasha a shekara mai zuwa (2018) a ranar Litinin mai zuwa 28 ga watan nan da muke ciki ne kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles za ta kece raini da kungiyar kwallon kafa ta Kamaru.  Wasannin za su gudana ne gida da waje inda a ranar Asabar 2 ga watan gobe ne kuma Super Eagles za ta kai wa Kamaru ziyara don yin wasa karo na biyu.

Wadannan wasanni biyu ne za su tantance ko Najeriya za ta haye gasar cin kofin duniya ko a’a.  Kawo yanzu dai Najeriya ce take saman tebur a rukunin B inda ta hada maki 6 daga wasanni biyu sai Kamaru da ke biye da maki 2 daga wasanni 2 yayin da Zambiya da Aljeriya suke da maki daidai a wasanni biyu.

Idan Najeriya ta samu nasara a wasanni biyun da za ta yi da Kamaru, za ta hada maki 12 kenan da hakan zai ba ta damar hayewa gasar cin kofin duniya da zai gudana a Rasha a badi amma idan Kamaru ce ta samu nasara a wasannin biyu, to za ta shiga gaban Najeriya inda za ta hada maki 8 yayin da Najeriya kuma za ta kasance da maki 6 da hakan zai nuna akwai matsala.

Tuni kocin Super Eagles Gernot Rohr ya gayyato ’yan kwallon da za su kara da Kamaru kamar yadda kocin Kamaru shi ma ya gayyaci nasa ’yan kwallon.

Idan za a tuna a watan Yunin da ya wuce ne kasar Afirka ta Kudu ta lallasa Najeriya da ci 2-0 a gida a gasar neman hayewa cin kofin Afirka da hakan ya bakanta ran da yawa daga cikin magoya bayan kungiyar Super Eagles inda wasu suka rika shakkun da wuya Eagles ta iya lallasa Kamaru a wasannin da za su yi.

Yanzu dai masoya kwallon kafa a Najeriya da Afirka da ma duniya sun zuba ido su ga yadda wadannan wasanni za su kasance, yayin da wasu ke ganin Najeriya ce za ta samu nasara, wasu suna ganin komai zai iya faruwa musamman a bangaren wasan kwallon kafa.