A gobe Asabar 26 ga watan Oktoba ne ake sa ran za a yi wasa mafi zafi a gasar rukunin La-Liga na Sifen a tsakanin kungiyar FC Barcelona da kuma ta Real Madrid.
A tarihin kwallo, babu kwallon da ya fi zafi kamar na wadannan kungiyoyin kwallon kafa biyu a duk lokacin da suka hadu. Hasalima daukacin duniya kan zuba ido su ga yadda wasan zai kaya.
Za a yi wasan ne da misalin karfe biyar na yammacin Najeriya kuma ana sa ran gidajen kallon kwallo a ciki da wajen Najeriya za su cika makil don kashe kwarkwatar ido.
A halin yanzu FC Barcelona ce take saman tebur da maki 25 daga wasanni takwas da ta yi, yayin da Real Madrid take ta uku da maki 22 daga wasanni 8 da ta yi.
Za a buga wasan ne a filin wasa na FC Barcelona watau Camp Nou.
Gasar La-Liga: Gobe FC Barcelona za ta kece-raini da Real Madrid
A gobe Asabar 26 ga watan Oktoba ne ake sa ran za a yi wasa mafi zafi a gasar rukunin La-Liga na Sifen a tsakanin…