✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar gudu

Wani matashi ne ya saba da gudu a babur, rannan ya tafi gun aiki, inda ya kai kilomita 25. Ya yi tafiyar da ta kai…

Wani matashi ne ya saba da gudu a babur, rannan ya tafi gun aiki, inda ya kai kilomita 25. Ya yi tafiyar da ta kai kilomita 23, saura kilomita biyu kawai ya isa, kawai sai suka yi kiliya da wani matashi, shi ma yana tika gudu a nasa babur din. Yana ganin wannann matashi da yake gudu, kawai sai ya yi kwana ya bi shi. Da wancan ya waigo ya ga an biyo shi da gudu, sai ya kara wuta, domin kuwa bai son a wuce shi. Nan fa suka runtuma, suka yi ta gasar tsere a tsakaninsu. Sai da suka ci kilomita 20, sannan ya samu wuce shi, daga nan ya juyo domin tafiya wajen aikinsa. Ya ce: “Haba, ai da ban wuce shi ba, sai ya yi ta kurin shi mai gudu ne.”
Sunusi Uban Kulob Garko Kano 07038766018