✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar Firimiyar Ingila: Jibi Chelsea za ta hadu da Arsenal, Manchester United da Eberton

A ci gaba da gasar rukunin firimiyar Ingila, a jibi Lahadi 17 ga wannan wata da muke ciki ne kulob din Chelsea zai barje gumi…

A ci gaba da gasar rukunin firimiyar Ingila, a jibi Lahadi 17 ga wannan wata da muke ciki ne kulob din Chelsea zai barje gumi da na Arsenal a wasa karo na biyar. Wasan zai gudana ne a filin wasa na Chelsea da ake wa lakabi da Stamford Bridge da misalin karfe 1 da rabi na rana agogon Najeriya.

Kawo yanzu kulob din Chelsea ne na uku a jerin kungiyoyin da ke fafatawa a gasar bayan ta hada maki 9 a wasanni hudu yayin da kulob din Arsenal kuma yake matsayi na 11 bayan ya hada maki 6 a wasanni 4.

A daya wasan kuma, kulob din Manchester United ne zai kece raini da na Eberton da misalin karfe hudu na yamma agogon Najeriya.

Kawo yanzu Manchester United ce take jan ragamar gasar bayan ta hada maki 10 a wasanni hudu yayin da Eberton take matsayi na 16 bayan ta hada maki 4 a wasanni 4.

Masu sha’awar kwallon kafa za su kashe kwarkwatar idanu kasancewa dukkan wadannan wasanni ne masu zafi kuma ana sa ran gidajen kallon kwallo za su cika makil don ganin yadda wasannin za su kaya.