✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gasar cin kofin Afirka na mata: Gobe Kamaru za ta hadu da Najeriya a wasan karshe

A Gobe Asabar idan Allah Ya kaimu, kasar Kamaru mai masaukin baki za ta kece raini da Najeriya a wasan karshe na gasar cin kofin…

A Gobe Asabar idan Allah Ya kaimu, kasar Kamaru mai masaukin baki za ta kece raini da Najeriya a wasan karshe na gasar cin kofin kwallon kafa na Afirka bangaren mata.
Ana gudanar da gasar ce a kasar Kamaru kuma Kamaru ta kai matakin wasan karshe  ne bayan ta lallasa kasar Ghana da ci 1-0 a wasan kusa da na karshe (Semi Final)  yayin da Najeriya kuma ta kai wasan karshe bayan ta lallasa kasar Afirka ta Kudu da ci daya mai ban haushi.
Najeriya ce mai rike da kambun, kuma ta lashe wannan gasa har sau bakwai a jere don haka idan ta samu nasara a wasan na gobe, za ta lashe sau takwas kenan a jere.
An fara gasar ta bana ce a ranar 20 ga watan Nuwamban, 2016 inda ake sa ran za a kammala a gobe Asabar 3 ga Disamba, 2016.  kasashe takwas ne suka fafata a gasar da suka hada da Kamaru da Ghana da Kenya da Najeriya da Afirka ta Kudu da Zimbabwe da Masar da kuma Mali.