A gobe Asabar za a yi bikin mika kyaututtuka ga zakaru uku da suka yi zarra a gasar rubutun kirkirarrun labarai na Hausa da Aminiya-Trust da hadin gwiwar kamfanonin Gandun Kalmomi da Open Arts suka gabatar a 2020.
Bikin wanda zai gudana da misalin karfe bakwai na dare, a Hotel 17 da ke Kaduna zai kuma a yaba wa wasu mutum 12 da suka yi kokari a gasar.
Da yake gabatar da zakarun, Shugaban Kwamitin Shirya Gasar, Farfesa Ibrahim Malumfashi ya bayyana cewa, “Kamar yadda aka sanar, aka kuma yi alkawari a farkon gabatar da wannan gasa, an shirya ta ce domin bukatar samar da ingantattun labarai na nishadi cikin Hausa da suke kunshe da matsalolin da suke jibge a tsarin dimokuradiyya da dambarwar siyasa a Najeriya.
“Wadannan labarai bayan kammala gasar, kuma an buga su a matsayin littafi, kuma ana sa ran su zama wata hanya ta nusar da jama’a, musamman matasa kan muhimmancin da ke tattare da inganta tsarin dimokuradiyya da tsabtace siyasar kasa baki daya.”
Shin su wane ne gwaraza kuma zakaru uku da a cikinsu za a fitar da zakaran-zakaru a gobe Asabar? Yaya sunansu, daga ina suka fito kuma ta yaya suka fara harkar rubutu?
Ga bayani a kansu nan kamar haka:
Mubarak Idris Abubakar
Matashi ne da aka haife shi a 1994 a Jihar Kano. Ya yi makarantar firamare da sakandare a Kano.
A yanzu kuma yana karatu ne a Kwalejin Koyon Aikin Kiwon Lafiya da ke garin Kankiya, a Jihar Katsina.
Ko yaushe ne hazikin matashin ya fara rubutu?
Ya ce: “Na fara rubutu ne tun a shekarar 2010, lokacin ina aji uku a karamar sakandare.
“Ina rubuta kirkirarrun labarai da fina-finai. Ya zuwa yanzu na rubuta littattafai da dama, sai dai har kawo yanzu ba wanda ya shiga kasuwa; sai dai suna kan hanya. Fina-finai kuwa, zuwa yanzu akalla na rubuta guda goma zuwa sama.”
Ko me ya ja ra’ayin gwarzon marubucin ya zabi ya zama marubuci?
Malam Mubarak ya ce: “Na zabi in zama marubuci ne, domin ta haka ne zan aika sakona inda ba lallai in je ba, har in koma ga Allah, ko kuma in ce ba lallai wani ya saurare ni ba ma. Amma rubutuna kadai yana iya fansata, wajen cimma burina na kawo gyara a cikin al’umma.”
Kafin samun wannan nasara ta Gasar Aminiya, ko an taba karrama ka a sanadiyyar rubutu?
Matashin ya amsa da cewa: “Na samu karramawa daga kungiyoyi irin su, Arewa Entertaiment and Media Concept da kuma Mujallar Zauren Marubuta, sai kuma ga shi Allah Ya huwace, babban gidan jarida na Media Trust Limited, mai wallafa jaridun Daily Trust da Aminiya, zai karrama ni a gobe Asabar.”
Labarinka mai taken “Tufka da Warwara” ya samu nasarar zama daya daga cikin uku da suka yi zarra, ka yi mana bayani takaitacce game da kunshiyarsa.
“Tufka da Warwara, labarin wani Gwamna ne da ya kammala wa’adin mulkinsa amma yana kyashin ya sakar wa mataimakinsa kujerar, domin ya gaje shi; duk kuwa da cewa mutane na son sa.
“Kan haka sai ya yi amfani da tuggu da lissafi irin na siyasa, ya kifar da shi; ya dora wanda yake ganin zai ba shi damar cimma burinsa. Sai dai hakan ya faskara, inda labari ya sha bamban.”
Rufaida Umar Ibrahim
An haifi Rufaida Umar ce a Kano, ranar 16 ga Janairun 1995. Ta yi makarantar firamare har zuwa sakandare a Kwalejin ’Yandutse.
A yanzu haka, tana karatu a ajin farko, a Kwalejin Ilimi ta Tarayya da ke Kano. Tana da aure kuma Allah Ya albarkace ta da ’ya’ya biyu.
Ko me ya ja hankalin gwarzuwa Rufaida zuwa ga fara rubuce-rubuce?
Ta amsa da cewa: “Yawan karance-karance ne ya ja ra’ayina na soma rubutu. Tun ina yi a takarda har dai a shekarar 2014 na rubuta wani labari da na yi wa take da “Mahaifiya.” Na saka wannan labari a wani dandali na Facebook.
“Ganin yadda mutane suka karbi rubutun a Intanet da kima, shi ya sa na ci gaba da yi. Alhamdu lillahi, zuwa yanzu na rubuta labarai fiye da goma.”
Sai dai marubuciyar ta ce ba ta taba wallafa cikakken littafi ba. Amma ta ce, “Ina dai fatar yin hakan a gaba, in Allah Ya yarda.”
Tunda kika fara rubutu, ko kin taba samun karramawa a sanadiyyarsa?
Ta ce: “A shekarar 2019, na samu karramawa daga Kungiyar HAF, Kano. Haka kuma Kungiyar Marubuta ta Najeriya (ANA), reshen Jihar Kano ta gayyace ni taron ganawarsu da marubuta.
“A shekarar 2020 kuma na shiga Gasar Hikayata ta BBC Hausa, inda labarina ya yi nasarar zama na uku. Wadannan duk wasu nasarori ne da na samu a dalilin rubutu.”
Ga shi cikin ikon Allah, labarinki na “Dimokuradiyyar Talaka” ya kasance daya daga cikin fitattun labaru uku da suka yi zarra a Gasar Aminiya, ki yi mana bayani takaitacce a kansa.
Rufaida ta ce: “Wannan labari ne game da wani matashi mai suna Rabi’u, wanda ya tsoma kansa cikin harkar siyasa. Sai dai a karshe lamura suka juye, sabanin tunaninsa; wanda ya yi silar rusa dukkan mafarkansa.”
Ubaida Usman
An haifi Ubaida Usman a 1992. Ita ’yar asalin Jihar Sakkwato ce kuma a cikin garin Sakkwato aka haife ta.
Ta yi makarantar firamare da sakandare a garin Sakkwato. Ta yi karatun digiri a Jami’ar Usman Dan Fodiyo, Sakkwato, inda ta yi nazarain Hikimar Koyarwa da Hausa (B.A. Ed. Hausa).
Ta kammala jami’a a shekarar 2016. Ta kasance mai sha’awar karance-karance da rubuce-rubuce sosai.
Ta rubuta littafi mai suna “Ra’ayin Masu Karatun Hausa Dangane da Hausa.” Ta ce babban burinta shi ne, ta ci gaba da fito da tunaninta a rubuce.
Tun yaushe gwarzuwa Ubaida ta fara rubutu?
Ta amsa da cewa: “Na fara rubuce-rubuce a dandalin “Amsoshina” a wani shafi na Facebook mai suna Makerar Sarrafa Harshe, wanda aka kirkira a shekarar 2012.
“Da muka samu ci gaba zuwa bude kafar Intanet tamu ta kanmu, Amsoshi.com a shekarar 2016, na ci gaba a matsayin Karamar Edita. Ya zuwa yau, ba zan iya kididdige adadin rubuce-rubucen da na tantance ba kafin a dora a shafin.”
Tunda farko ma, me ya ja ra’ayinta ga harkar rubutu?
Gwarzuwar ta Aminiya ta amsa da cewa: “Abin da ya ja ra’ayina game da rubuce-rubuce shi ne, ina son karatun littattafan Hausa.
“A kan haka ne na ga ya kamata in fito da irin nawa tunanin. Ina cikin Kungiyar Amsoshi Writers, a karkashin Amsoshi Language Service.
“Na samu nasarori da dama, ko kasancewata a cikin masu tantance rubuce-rubuce kafin a dora a kafar Amsoshi, shi ma nasara ce.
“Ga kuma wannan damar da Allah Ya ba ni ta samun shiga cikin gwarazan Gasar Gajerun Labarai ta Aminiya. Ita ma wannan nasara ce babba da kowane marubuci ke fatar samu.”
Labarinki mai taken “Ranar Kin Dillanci” ya samu nasarar zama daya daga fitattu uku a gasar, ki dan yi mana takaitaccen bayani a kansa.
“Ranar Kin Dilllanci, labari ne da aka gina shi kan jigon jan hankalin shugabanni, su gane cewa ba kullum ake kwana a gado ba, sannan duniya ba matabbata ba ce.
“Duk mukamin mutum da karfin ikonsa, akwai ranar da zai mutu. Da zarar mutuwa ta riske shi kuwa, karfin mulkin ya kare.
“Baya ga haka, labarin ya tabo al’amarin fyade a matsayin wani babban al’amari da ke ci wa al’ummar yau tuwo a kwarya. Labarin ya nuna halin ko-in-kula da wadansu shugabanni ke yi dangane da al’amarin fyade.”