Hukumar Kula Da Al’amuran Sadarwa ta Najeriya (NCC) ta ce tana nuna damuwa sosai da yadda kamfanonin sadarwa a kasar nan suke tafiyar da tsarinsu, don haka gasa a tsakaninsu za ta rage farashin tu’ammali da tarho ga mutane.
Darakta mai kula da al’amuran jama’a na Hukumar NCC, Tony Ojobo ne ya bayyana haka a garin Obollo-Afor, Jihar Inugu, a yayin gudanar da taron masu ruwa da tsaki da hukumar ta shirya a garin.
Ojobo, wanda ya samu wakilcin Shugaban Harkokin Watsa Labarai na hukumar, Reuben Mouka ya ce, “A matsayinmu na masu kula da harkar, ba mu tsoma baki wajen daidaita farashin yau da kullum. Abin da muke yi shi ne, muna bayar da ka’idar tazarar da farashi zai samar ga kamfanoni, wanda ba za su ketare haka ba.
“Abin da mukan yi shi ne, mu tabbatar an samu gasa tsakanin kamfanonin, wanda haka zai sanya farashi ya sauko. Domin a duk lokacin da wannan kamfani ya kara farashin data, mutum zai iya zuwa wani kamfanin, inda zai iya samun rangwame.
“Muna nan muna shirin ba kamfanonin sadarwar umurni, domin su rika jaddada kimar hajarsu kai tsaye koda data ta kare nan take, za ka iya cin gajiyarta nan da makonni biyu, wanda haka zai taimaka wa abokin hulxa.
Shugaban karamar Hukumar Udenu, Mista Frank Ugwuanyi, a yayin da yake tattaunawa da manema labarai, ya shawarci kamfanonin sadarwa da su rika biyan haraji ga kananan hukumomi, inda suka girke na’urorinsu.