✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gas din girki ya fashe ya kashe mutum 8 a Katsina

Fashewar gas din girki ya yi sanadiyyar mutuwar mutum takwas dukkan su ‘yan gida daya a cikin garin Dan Musa da ke Karamar Hukumar Dan…

Fashewar gas din girki ya yi sanadiyyar mutuwar mutum takwas dukkan su ‘yan gida daya a cikin garin Dan Musa da ke Karamar Hukumar Dan Musa ta jihar Katsina.

Ga s din ya fashe ne lokacin da ake girki da shi, kuma gobarar ta faru ne da misalin karfe 5 na yamma ranar Asabar lokacin da daya daga cikin wadanda suka rasu take girki a cikin gida.

Rahotan bai tantance sunayen wadanda suka rasu ba, sai makwabtan gidan da abin ya faru sun bayyanawa manema labarai cewa, a cikin wadanda suka rasu akwai matan aure uku da yara biyar.