Al’ummomin da ke zaune a gundumomin Baraza da Durr a Karamar Hukumar Dass da ke Jihar Bauchi, sun koka game da yadda garkuwa da mutane ta kankama a yankin inda hakan ya sanya su zaman dar-dar.
Mutanen yankin sun shaida wa Aminiya cewa a bara an kashe musu mutum biyu, wani malamin asibiti da aka harba, da kuma dan majalisar da ke mazabar Dass a Majalisar Dokokin Jihar Bauchi, marigayi Musa Mante Baraza.
- An cafke dillalin makaman ’yan bindiga a Zamfara
- Mahara sun yi awon gaba da matar Dagaci a Kebbi
- Yadda dubun mai yi wa yara maza fyade ta cika
Sun ce tun lokacin da aka kashe dan majalisar, aka dauki matansa biyu da dansa, sai masu garkuwa da mutanen suka ci gaba da zuwa yankin daga lokaci zuwa lokaci suna yi musu dauki dai-dai su tafi da su daji sai an biya kudin fansa.
Al’ummar sun koka cewa kwanakin baya an kama mutum uku da ake zargi da kashe dan majalisar kuma hakan ya sa sun samu saukin garkuwa da mutane, amma sai suka ji cewa an sake su tun kafin a kai su kotu.
Majiyar Aminiya ta ce mutanen garin Durr sun kasance a tsorace tun lokacin da aka kashe dan majalisar.
Majiyar ta ce sata da garkuwa da mutane na bayan-bayan nan da aka yi a yankin su ne wadanda aka sace mutum hudu, dan Mai Gundumar Durr wanda makaho ne da kuma wadansu mata uku.
Masu garkuwan sun shiga gidan Mai Gundumar Durr, da suka ga ba ya gani sai suka doke shi, kuma suka dauke babban dansa.
Da za su tafi sai suka bar fitilu masu haske a kunne a kusurwa uku don su yaudari dukkan wadanda za su kawo dauki don su dauka suna kwance ne suna haskawa, sai da safe aka gane hasken ne kawai amma sun tafi.
Majiyar ta ce a wannan dare, masu garkuwar sun shiga gidan wani dattijo suka sassare shi suka tafi da matarsa wacce sai da aka biya Naira dubu 50 aka karbo ta.
Sannan suka kwace babura biyu na wadanda suka je karbo ta.
Inda ake boye wadanda aka sace
Da yawa daga cikin wadanda suke karbo wadanda aka yi garkuwa da su, sun shaida wa Aminiya cewa sun karbo su ne a Dutsen Kardam, wani babban dutse da ke cikin Karamar Hukumar Tafawa Balewa. Sun ce dajin da dutsen ke ciki kungurmin daji ne.
Sun ce ba su kadai ne wannan lamari ke faruwa da su ba, har ma da kauyukan makwabta, inda a makon jiya masu garkuwar shiga garin Yalwan Bashi suka sace wata mata, kuma da mutane suka bi su suna jifar su har sai suka rika magana da yaren mutanen yankin cewa su rabu da matar kada a kama su, shi ne suka gudu.
Abin da ’yan sanda ke yi
Kakakin Rundunar ’Yan sandan Jihar Bauchi, SP Mohammed Ahmed Wakil ya ce a Jihar Bauchi ’yan sanda suna kokari wajen kama masu garkuwa da mutane.
“Ana kama wadanda suke aikata laifi a duk lokacin da suka yunkuro,” inji shi.
Sai ya roki jama’a su rika kai rahoton duk wani batagari da suka gani ko wadanda ba su yarda da su ba ga ’yan sanda.
Wakil ya yi alkawarin bincikar abin da ke faruwa a yankin Dass daga shugabannin ’yan sanda da ke kula da yankin, kafin ya yi wa waklilinmu cikakken bayani.
Sai dai har zuwa lokacin hada wannan rahoto wakilinmu bai samu karin bayanin ba.
A lokacin ziyarar da Gwamna Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya kai kananan hukumomin Dass da Toro, ya nana kudirin gwamnatinsa na kare rayuka da dukiyoyin jama’a.
Gwamna Bala Mohammed ya hori sarakuna da al’umma su kula da bakin da za su zo su zauna da su don fahimtar halayensu da kuma kai rahoton duk wanda ba su yarda da shi ba ga hukuma.
‘Kwadayi ke jefa matasa aikata laifi’
Wani tsohon Kwamishinan ’Yan Sanda da ya bukaci a sakaya sunansa, ya ce aikata laifi yana tafiya ne tare da rayuwar dan Adam, “A kowane lokaci ba a rasa masu aikata laifi cikin al’umma,” inji shi.
Sai ya danganta lamarin da talauci da rashin aikin yi da karancin jami’an tsaro da karancin kayan aiki da mutuwar zuciyar matasa da kwadayi da son tara abin duniya.
Ya shawarci gwamnati ta kara kaimi don warware wadannan matsaloli domin a samu saukin lamarin.
Ya kuma shawarci jami’an ’yan sanda da su kara kokari wajen neman bayanan sirri da bin didigin lamurra domin shawo kan matsalolin tun ba a aikata su ba.