✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Garkuwa da mutane:  Matasa sun tare titi a Kaduna

Rundunar ’Yan sanda Jihar Kaduna ta ce ta samu nasarar dawo da doka da oda a kan titin Nnamdi Azikwe  bayan da wadansu fusatattaun matasa…

Rundunar ’Yan sanda Jihar Kaduna ta ce ta samu nasarar dawo da doka da oda a kan titin Nnamdi Azikwe  bayan da wadansu fusatattaun matasa suka rufe hanyar don nuna fushinsu game da yadda ake yawan garkuwa da mutane a sassan jihar.

Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya ya ruwaito cewa da misalin karfe 1:00 na dare wadansu da ake zargin ’yan bindiga ne suka mamaye yankin Nariya kusa da Kabala suka yi awon gaba da mutane ba tare da an kama ko daya daga cikinsu ba, abin da ya haifar da zanga-zangar.

Wani mazaunin yankin, Abubakar Ladan, ya ce lamarin ya rutsa da mata uku da saurayi da kuma wani magidanci.

Kakakin ’Yan sandan Jihar DSP Yakubu Sabo ya tabbatar da faruwar lamarin.

Sabo, ya ce lokacin da aka sanar da  ’yan sandan yankin faruwar lamarin nan take DPO da ke yankin ya jagoranci ayarin jami’ansa domin kai dauki.

“Lokacin da ’yan sanda suka isa wurin tuni ’yan bindigar sun tsere.  Ya ce maimakon mutane su ba ’yan sandan hadin kai sai suka shiga yin zanga-zanga har ta kai ga tare babbar hanyar.

Ya ce tare babbar hanya irin wannan ba daidai ba ne domin hanya ce da ta hade jihohin Najeriya.

“A duk lokacin da kake bayyana bacin ranka, to kada ka shiga hakkin wadansu, ta hanyar tare wata hanya don kada a wuce,” inji shi.

Ya ce abin bakin ciki shi ne yadda matasan suka nufi ofishin ’yan sanda a yayin zanga-zangar da nufin konawa.

Rundunar ta ce an kama wadansu daga cikin masu zanga-zangar kuma da zarar an kammala bincike za a kai su kotu don a zartar musu da hukunci.

Daya daga cikin wadanda aka kama, ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya (NAN) cewa matasan sun harzuka ne ganin ’yan sanda ba su kai dauki da wuri ba a lokacin da al’amarin yake faruwa.