✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamnatin Tarayya ta soke kwangilar aikin titin Abuja-Kaduna

An shafe sama da shekara shida ana aikin titin amma ba a kammala ba.

Gwamnatin Tarayya ta soke kwangilar da ta bai wa Kamfanin Julius Berger don yin aikin titin Abuja zuwa Kaduna da Zariya zuwa Kano.

Wannan matakin ya biyo bayan rashin amincewar kamfanin na halartar taron da za a yi don kammala tantance sabon kuɗin kwangilar da za a biya wanda ya kai Naira biliyan 740.

Julius Berger, ya nemi a yi sauye-sauye a kwangilar amma rashin halartar su taron, ya sa gwamnatin soke kwangilar da ta ba su.

A cewar Daraktan Yaɗa Labarai na Ma’aikatar Ayyuka ta Tarayya, Mohammed Ahmed, Julius Berger bai bi sabon tsari da kuɗin da za a biya don kammala aikin.

A cewarsa kamfanin ya dakatar da aikin titin duk da umarnin da gwamnati ta ba shi.

Ma’aikatar ta bai wa kamfanin wa’adin kwanaki 14 kafin soke kwangilar.

An fara bai wa Julius Berger kwangilar ne a 2018 a kan Naira biliyan 155.7 tare da wa’adin kammala aikin cikin shekara uku.

Amma kuɗin aikin ya ƙaru zuwa sama da biliyan 600, duk da cewar an shafe shekara shida ba tare da kammala rabin hanyar ba.

Ma’aikatar ta shafe sama da shekara ɗaya tana tattaunawa da kamfanin don nemo mafita, amma ba a cimma yarjejeniya ba.

An sake tsara fasalin yadda aikin zai kammala, wanda za a yi amfani da simintin Dangote wajen gyaran wani ɓangare na titin da kuma gyaran kilomita 38.

An bai wa Julius Berger aikin kammala sauran titin mai tsawon kilomita 127, amma yanzu an soke kwangilar sakamakon rashin cimma yarjejeniya da Gwamnatin Tarayya.

Gwamnatin na fatan sauyin zai inganta ci gaban aikin titin tare da sauƙaƙa zirga-zirgar masu amfani da hanyar.