✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Garkuwa da mutane a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya ta yi kamari

Garkuwa da jama’a a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya tana kara ta’azzara, inda matafiya kan shiga matsala. A Larabar da ta gabata ne masu garkuwa…

Garkuwa da jama’a a kan hanyar Kaduna zuwa Zariya tana kara ta’azzara, inda matafiya kan shiga matsala. A Larabar da ta gabata ne masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa suka yi garkuwa da wata mata mai juna-biyu.

Mijin matar, Murtala Marabar-Jos ya ce, “Abin ya faru ne yayin da iyalansa suke dawowa daga Katsina, inda suka je gaisuwa. Da suka baro barikin sojoji da ke garin Jaji da ke Jihar Kaduna, kafin su isa garin Birnin-Yero sai suka hangi sojoji suna daga masu hannu a daidai gonar Sambawa. Da suka tsaya da misalin karfe takwas da rabi na dare, sai suka lura cewa masu garkuwa da mutane ne, inda suka saukar da matata mai juna-biyu da ya kai wata shida da kuma kaninta Abdul’aziz, suka ce wa direban ya wuce, bayan sun nuna masa bindiga da muggan makamai.

“Suka tafi da su kungurmin daji a kasa, sannan suka kwace Naira dubu daya na Abdul’aziz suka je suka sayo masu lemon kwalba da biredi, wanda shi suka yi ta ci har na tsawon kwanaki uku, kafin aka fanshe su daga hannun Fulani masu garkuwa da mutane, bayan an ba su fiye da Naira miliyan daya.”

Malam Murtala, wanda direba ne a Marabar Jos ya ce, “An karbi kudin ne a daidai tudun jar kasar nan da ke tsakanin Birnirn Yero da Marabar Jos. Kuma da kyar da jibin goshi dangi da abokan arizki da sauran jama’a hada suka biya wannan kudi na fansa. Sannan su kuma aka sallamo su a wani bangare daban.”

Ya kara da cewa ya zuwa yanzu, masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa sun sace mutane sun kai biyar a tsakanin Birnin Yero da Marabar-Jos da kuma Rigachikun da suka hada da Alhaji Abubakar E.S. da sauransu, inda akwai wanda suka shiga cikin gidansa suka dauke shi da karfin tsiya, suka tafi da shi har sai da aka biya fansa suka sako shi.

Bugu da kari ya ce da suka shaida wa ofishin ’yan sanda da ke Rigachikun, sai suka ce ba su da makamin da za su tunkari masu garkuwa da mutanen. Wakilinmu ya yi kokarin tuntubar Kakakin rundunar ’yan sanda a Jihar Kaduna, ASP, Aliyu Hussaini Mukhtar ta waya, domin jin ta bakin hukumar, amma hakarsa ba ta cin ma ruwa ba.

A wani labarin makamancin wannan, a daren Talatar da ta gabata, masu garkuwa da mutane don neman kudin fansa sun shiga gidan dan jarida mai aiki da gidan Rediyo Nagarta da ke Marabar-Jos Kaduna, Malam Nasir Yakubu Birnin Yero, da karfe daya da rabi na daren Talata, inda suka dauke matarsa da ’yarsa, suka tafi da su.