✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Satar dalibai yunkuri ne na lalata ilimi a Najeriya —MSSN

Kungiyar ta yi kira da a kawo karshen yon garkuwa da mutane.

Kungiyar Dalibai Musulmi ta Najeriya (MSSN) ta ce satar dalibai a wasu sassan Najeriya wata dabara ce ta hana neman ilimi.

Shugaban kungiyar MSSN na kasa, Malam Shehu Usman Abubakar, ne ya dalibai da dama sun daina zuwa daga makaranta saboda yawaitatr garkuwa da mutane.

  1. An sauke Firaiministan Tunisia Hichem Mechichi daga mulki
  2. Masu garkuwa sun koma karbar kudin fansa ta banki a Abuja

A cikin wata sanarwa a ranar Asabar, a Birnin Kebbi, Malam Shehu ya ce ilimi shi ne babban tushen cigaban kowace kasa da al’umma a duniya.

“Kamar yadda satar mutane ta fara shafar makarantu, mu, a matsayinmu na MSSN, muna kallon hakan a matsayin wani yunkuri na hana neman ilimi, musamman a Arewacin kasar nan.

“Saboda haka, ya kamata a yi abin da ya dace domin dakatar da hakan cikin gaggawa,” inji shi.

Abubakar ya bukaci gwamnatoci a dukkan matakai da su kara kaimi wajen tabbatar da kare rayuka da dukiyoyin ’yan kasa, yana mai cewa yawan aikata laifuka yana da ban tsoro, musamman fashi da garkuwa da mutane.

A cewarsa, hukumomin tsaro sun yi rawar gani wajen yaki da rashin tsaro, yayin da ya yaba wa Gwamnatin Jihar Kebbi kan kokarin da take yi na ceto daliban Kwalejin Gwamnatin Tarayya da ke Birnin-Yauri.

“Muna rokon sauran gwamnatocin jihohin da abin ya shafa su bi sahun Gwamna Atiku Bagudu,” inji shi.

Shugaban na MSSN ya kuma bukaci Musulmi da su koma ga Allah Madaukaki cikin tuba kuma su kasance masu addu’a don inganta Najeriya.