Barkanmu da Sallah Manyan gobe, tare da fata nana cikin koshin lafiya. A yau na kawo muku labarin ‘Garba mai satar naman layya’. Labarin ya yi nuni ne ga illar da nama ya yi wa Garba. A sha karatu lafiya.
Taku; Amina Abdullahi.
A safiyar ranar Sallar layya ne bayan mahaifin Garba da mahaifiyarsa tare da kannensa sun tafi sallar idi kamar yadda suka saba a kowace idi. Garba na sanye da sabon tufafi shadda fara wacce mahaifinsa ya xinka masa a karamar sallar da ta gabata.
Tun da suka isa masallaci mahaifin Garba ya lura da irin farin cikin da yake ciki har mahaifinsa ya tambayesa ko mene ne dalilin wannan farin ciki?
Garba ya ce babu abin da ya fi burge shi kamar yadda ake cin namar layya a babbar sallah. Sai mahaifinsa ya yi dariya tare da cewa yawan cin nama na sanya ciwon ciki. Daga nan bayan an gabatar da sallar Idi mai raka’a biyu suka koma gida.
Suna isa gida mahaifinsu ya kamo rago ya yanka aka kasatfa nama. Kasancewar mahaifin Garba na da mata huxu kuma shi mai karamin hali ne, da aka gama yanka sai ak ayi kasafta gida huxu bayan an ware na sadaka.
Kowace mata sai ta xan tsakurawa xanta yanka biyu sauran kuma aka yi girki da shi aka soya wasu aka ajiye. Wannan abu bai yi wa Garba daxi ba da hakan ya sa ya shiga xakin mahaifiyarsa ya cinye kusan rabin naman da ta ajiye a saman tebur.
Da yamma sai cikin Garba ya ruxe ya shiga yin amai da gudawa da hakan ta sa iyayensa ba su yi bacci ba aka kai shi asibiti aka rika yi masa allurai. A karshe dai haka aka gama Sallar ba tare da Garba ya warke daga ciwon ba.
Manyan gobe ku zama masu tawakkali a kowane hali da kuka tsinci kansu da kuma yin godiyar Allah.