A makon da ya arce Jiga-jigan jam’iyya mai dan boto da sanda jirge suka shirya wani gangamin tara damin Hauro ga Shugaban Gudun-loko da Jona-tantin mulki, kuma an yi nasarar samun garabasar gararumar Hauro gashin balama karamin lauje da sili. Wannan al’amari dai a daukacin tarihin kasar Haurobiya ba a taba tara gararumar wasan Samson-siya-siya a tsarin dama-dama da-kurda-kurdar damo-da-kura-diyya.
Hakika Haurobiyawa sun dugunzuma cikin tashin hankali, a daidai wannan lokaci da ake cewa kasuwar mantunkuza ta yi warwas a kasuwanni duniya; sannan In-gwangwaje-in-wala ta gabatar da baje kolin Hauro na shekara ta dubu karamin lauje da sili da babban lauje a maujalisar kasa, inda a daidai wannan lokaci an fasko wasu samarin kusu da suka yi sabi zarce da Dalar Hauron Amurkawa, har gashin balama sili. Uwargida In-gwangwaje-in-wala ta bayyana cewa, ‘gangamijo damin Hauro tiren-taliya ko ma cikin tirela sun yi batan dabo.’ Kuma idan har ba mu ari faden Malam Mantau ba, kowa na sane da Damin Hauro gashin balama da Maimartaba masanin Sisi-da-sisi ya koka kan yadda Mace-da-zane da mukarrabantan gwamnatin Jam’iyya mai dan boto da sanda jirge suka jirge da su.
Hauroibiyawa, ba gararumar da aka tara wa Shugaban Gudun-loko da Jona-tantin mulkin mulaka’u ta dame ba, amma ina takaicin yadda idan talaka mai fama da talalar talauci ya saci akuya, sai kawai a garkame shi a gidan Yari, shi kuwa Yari ya yi masa sasarin yari da dan kunnen dabaibayin kwanaki barkatai. Da kuma a ce wani jibgege ne ya tsakuri kasonsa daga lalitar gwamnati, idan har ya samu gwanayen lauye-lauyen dokoki, sun san yadda za a wanke da sabulun salo, koda kuliya ya ki ya. Wani al’amarin mai daure kurungu gangam, shi ne, yadda Loma-a-murde ya zama muzurun lami, kamar yadda na sha bayyanawa kusan kowane darasi.
A irin wannan kasa da ake aiwatar da “tsarin kashin sha-kushe,” wato su gundumi fasa-kwanya su ne a koli, ’yan mitsil-mitsil kuwa a taushe su, suna ji, suna gani, ba za su iya katabus ba.
Uwa-uba sun yi rugu-rugu da Hauron Haurobiya, inda suka haifar da hauhawar farashin kayan motsa muka-muki, alhali sanin kowa ne da ruwan tumbi ake jan na kwakware.’ Irin wannan sagegeduwa da shagabanni masu hankali a hannun taguwa ke yi mana ya kai intaha.
Ina ganin Haurobiyawa sun dandana kudarsu a hannun mai dan boto da sanda jirge, don haka ba sa bukatar wani ya ce musu kad aku kada mata kuri’unku. Ina fata kow aya fahimci cewa daukacin dmain Hauron da ake yin sabi arce da su, ko samartakar kusu, du kana yi ne don miyagun bayi su samu ’yan matsabban holewa, a cikin da wajen Haurobiya. Irin wadannan migayu da zarar uwar jikinsu ta motsu, sai a zarce da su zuwa farfajiyar Bokan Turai t akasashen ketare; idan ’yan dugwi-dugwi dinsu suka bukaci koyon watsattsake a tafarkin Bobo da kwambon Bokoko, nan ma sai a kwashe su a kai su kasashen ketare, don su ketare wa tsallen badaken direbobin alli da jami’an asusun ilimi a daukacin jam’in jami’o’in Haurobiya.
Babban darasin da ni ke son ’yan makaranta su karanta a tsarin wannan manhaja mara hajijiya, shi ne, akwai tarin kazanta da aka jibge a jujin Haurobiya, kuma amtukar ba mu tashi haikan wajen tsaftace muhalli ba, to uwar jikinmu za ta ci gaba da jikkata.
Masu yaren Hau-hau wajen hawansa ba tare da sa-in-sa ba, sun furta cewa, “jiki magayi, shan tabar dan Korau.” Hakika ba ni da masaniya kan yadda dan Korau ya banki hayakin taba, ko ya yi yunkurin bulbule sama da hayaki, har ta shake shi. Babban lamari dai kowa ya sani cewa, a tsarin manahajar mu mara hajijiya, da tsarin tarayya da biyayyar al’umma akwai:
Tabba ta tabbata a barta
Amma wasu har batta suke yi mata
A bkain bata
Su yi kayan mota zuwa dambatta
Mutanen dambatta na san ba ku shan taba.
Wannan zance dai babu tababa!
Haurobiyawa kada mu yarda da masu yawon-dara da kwanyarmu, masu kiren zuki-ta-malle kama kare ka hada shi da zomo, don kawai su dare bisa karaga, su yi ta rangwada mana na aura. To mu yin a aura, don kada mu ci na aura. Mu kauce wa karbar gararumar gyaran jar miya, mu jajirce kan manufar tsinuwa ga samarin kusun da ke samfewa da adaka ko masu runton kujera.
Batu na ingarman karfen karafa, wannan gararumar Hauro gashin Balama karamin lauje da sili da mai dan boto da sanda jirge ta tara, kudi ne na wala-wala da aka jinka wa ’yan kungiyar Jona-tantin mulki. Kun ga ke nan, tunda gama-garin al’umma ba za su samu wata fa’ida da su ba, wajibi ne mu kyamace su. Idan kuma Mai-duka ya kaddara reshe ya juye da mujiya, kun ga sai an kwato wannan damin Hauro a zo a yi mana hidima a farfajiyar Bokan Turai da wurin koyon watsattsake da buda wagagen littattafai; a inganta sana’ar na-duke da limbu-limbu a cikin lambu.
Kada mu bari a sake kwata kidin jaujen da suka yi da gangunan jikkkunanmu. Mu share miyagu, mu yi juyin-juya hali, ta yadda za mu fida daga cikin duhun-dundumdurundum, ko a daina yi mana cin duhu. Haurobiyawa idan na-zomo ya ji, to gangar jiki ta tsira!
Gararumar Hauro gashin balama karamin lauje da sili
A makon da ya arce Jiga-jigan jam’iyya mai dan boto da sanda jirge suka shirya wani gangamin tara damin Hauro ga Shugaban Gudun-loko da Jona-tantin…