✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Gangar danyen mai 900,000 ake sacewa kullum a Najeriya —Lawan

Ya bukaci kasafin 2023 ya ba da muhimmanci wajen kammala manyan ayyukan ci gaban kasa

Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Ahmad Lawan, ya ce Najeriya na asarar gangar danyen mai 700,000 zuwa 900,000 kulli yaumin saboda ayyukan barayin mai.

Lawan ya ce barayin danyen mai su ne manyan masu kawo cikas ga cigaban Najeriya inda suke ja wa kasar asara kashi 35 cikin 100 na kudaden shiga daga bangaren mai da iskar gas.

Ya ce barayin danyen mai a Najeriya ya zama babban al’amari, “Makiyan kasa ne kuma sun yi damarar yaki da kasa. Don haka, dole a dauki mataki mai tsauri wajen yaki da masu sace man kasa.”

Sanatan ya fadi hakan ne a zauren Majalisa lokacin da Shugaba Buhari ya je gabatar da kasafin 2023 ranar Juma’a a Abuja.

Da yake jawabi, Lawan ya ba da tabbacin a shirye ’yan Majalisar Tarayya suke na su yi aiki wajen ganin an amince da kasafin kafin karshen wannan shekarar kamar yadda suka yi a baya.

Ya kuma bukaci kasafin 2023 ya ba da muhimmanci wajen kammala manyan ayyukan ci gaban kasa da ke gudana don amfanin kasa da al’ummarta.