Sanannen mai kama barayi wanda aka fi sani da suna Shanu Shehu Musa Aljan, ya ce babu amfani Gwamnonin Zamfara da Katsina su yi sulhu da ’yan ta’addan domin a cewarsa ganganci ne.
Ya kuma bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da manema labarai a jihar Kaduna dangane da nasarar da ya samu na kama wasu shanun sata da ya yi a jihar.
Aljan, ya kara da cewa ’yan ta’addan sun mallaki manyan makamai masu yawa, amma idan aka kama su, sai zo da batun yin sulhu.
” Barawo na da mutum kusan nawa a karkashinsa ya kawo maka bindigogi goma kai kuma ka tafi kana ihu wai kun yi sulhu da barayi ai wannan ganganci ne. Ni dai abin kunya ne a ce wai Gwamna ya cewa barawo ka yi hakuri. Ka zo a yi sulhu da kai.”

