✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje zai tallafa wa ‘yan Kasuwar Sabon Gari

Gwamnatin Jihar Kano za ta tallafa wa ’yan Kasuwar Sabon Garin Kano da gobara ta yi jawo musu asara a  bangaren masu sayar da kujeru…

Gwamnatin Jihar Kano za ta tallafa wa ’yan Kasuwar Sabon Garin Kano da gobara ta yi jawo musu asara a  bangaren masu sayar da kujeru da tebura da kuma wani rukuni na masu sayar da magunguna a makon jiya.
Gwamnan Jihar Dokta Abdullahi Umar Ganduje ne ya bayyana haka yayin da ya ziyarci bangaren da gobarar ta shafa, inda ya jajanta musu tare da bayyana matakan da gwamnati ke dauka wajen magance yawaitar tashin gobara a kasuwanni.
Ya ce tallafin da za a ba su ba wai yana nufin diyya za a biya su ba, sai dai za a rage masu radaddin asarar da suka yi ta dukiyoyinsu ta yadda za su ci gaba da harkokin neman abinci.
Gwamna Ganduje ya kuma sanar da cewa gwamnati za ta kafa dokar hana shan taba a cikin al’umma da wuraren kasuwanci domin kauce wa yawaitar tashin gobara, inda kuma ya bukaci ’yan kasuwar su hada hannu wajen samar da hanyoyin magance yawan tashin gobara da ake samu a kasuwanni.