Shugaban Buhari ya bayyana gamsuwarsa da yadda Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje ke ciyar da jihar gaba ta hanyar manyan ayyukan more rayuwa.
Buhari ya bayyana haka ne bayan ziyarar kaddamar da aikin titin jirgin kasa daga Kano zuwa Kaduna da kuma Gadar Dangi da ya bude a Kano.
- ‘Na shiga harkar fim duk da ana zagin masu yin ta’
- Masu juna biyu sun mutu wajen rububin karbar abinci a Borno
“Na zo Kano don gane wa idona irin ayyukan da Gwamna Ganduje ke yi kuma tabbas na gamsu na kuma yi farin ciki da abin da na gani.
“Jihar Kano ta yi zarra, za kuma ta iya gogayya da sauran jihohin duniya saboda jajircewar gwamnan wajen kammala ayyukan gwamnatocin baya tare da kirkiro wasu manya,” a cewar Buhari.
Buhari ya bayyana aniyarsa ta kara samar da abubuwan more rayuwa ga al’ummar Najeriya, musamman bunkasa harkokin kasuwanci da sauransu.
Bayan kaddamar da ayyukan da Buhari ya yi, a karon farko ya ziyarci Fadar Sarkin Kano tun bayan darewar Sarki Aminu Ado Bayero kan karagar mulki.
Daga nan ya zarce zuwa Jiharsa ta Katsina inda yake kaddamar da wasu ayyuka, a can kuma zai yi hutun Babbar Sallah.