✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ganduje ya yi ta’aziyyar mutanen Dambatta 16 da aka harbe

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje, ya jajanta bisa rasuwar mutun 16 ’yan asalin jihar da ’yan ta’adda suka bindige a kan hanyarsu ta zuwa Kano…

Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Ganduje, ya jajanta bisa rasuwar mutun 16 ’yan asalin jihar da ’yan ta’adda suka bindige a kan hanyarsu ta zuwa Kano daga Abuja.

“Mun kadu da samun labarin rasuwar mutum 16 ’yan asalin Karamar Hukumar Dambatta a hanyar Abuja-Kaduna, lokacin da suke dawowa daga Abuja zuwa Kano sakamakon harin da wasu ’yan ta’adda suka kai musu”, inji shi.

Wannan na kunshe ne cikin sakon ta’aziyar gwamnan ta hannun mai magana da yawunsa, Abba Anwar, ga dangin mutanen da harin ya ritsa da su a madadin gwamnati da jama’ar Jihar Kano.

Ganduje ya yi addu’ar “Allah Ya karbi shahadarsu, Ya kuma hukunta masu aikata irin wannan ta’addancin”, yana mai cewa “babu abun tashin hankali sama da wannan”.

Gwamnan ya bukaci jama’a da su dukufa wurin yin addu’o’in nema wa mamatan gafara da fatan Allah Ya ba wa ’yan uwansu hakurin rashin.