Gwamnan Jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya sasanta da daya daga cikin jiga-jigai bakwai da ake kira ‘yan G-7 a jam’iyyar APC a Jihar, Sanata Barau Jibrin, inda ya janye masa takarar kujerar Sanatan Kano ta Arewa.
Barau wanda ke zaman Shugaban Kwamitin Kasafin Kudi na Majalisar Dattawa, shi ne mai wakiltar mazabar Kano ta Arewa a majalisar a yanzu, kujerar da Ganduje ya nuna sha’awar tsayawa takara a 2023.
- Batanci: An kai wadanda ake zargi da kashe Deborah gidan yari
- Tsohon dan wasan Barcelona, Maxi Rolon ya mutu a hatsarin mota
Sai dai wasu majiyoyi sun ce a yanzu gwamnan ya yanke shawarar janye kudirinsa na tsayawa takarar Sanata tare da amincewa Barau ya koma zauren majalisar bayan yin sulhu a tsakaninsu.
Da ya ke tabbatar wa Aminiya yin sulhun, Sakataren jam’iyyar APC na Kano, Ibrahim Zakari Sarina, ya ce an samu nasara a zaman sulhun da aka yi tsakaninsu.
“Ana ci gaba da yin sulhun,” in ji shi dangane da rahotannin da ke cewa Ganduje ya amince Barau ya koma Majalisar Dattawan.
Aminiya ta rawaito cewa ‘yan G-7 wanda Sanata Ibrahim Shekarau ke jagoranta, sun sha takun saka da tsagin gwamnan Jihar kan shugabancin jam’iyyar, wanda ta kai ga zuwa kotu, lamarin da ya sanya Kotun Koli ta yi watsi da karar tare da bai wa Abdullahi Abbas shugabancin jam’iyyar.
Tuni wasu daga cikin masu takun saka da tsagin gwamnan suka sauya sheka zuwa jam’iyyar NNPP mai kayan marmari a Jihar, wanda shi kansa Sanata Malam Ibrahim Shekarau ke shirye-shiryen bin sahunsu.
Sai dai a makon da ya gabata Barau, ya dage kan cewa ba shi da wani shiri na ficewa daga jam’iyyar mai mulki kuma a shirye ya ke ya tsaya takarar Sanata a karkashin jam’iyyar.