Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano, ya nada Barista Mahmoud Balarabe, a matsayin mukaddashin Shugaban Hukumar Karbar Korafe-korafen Jama’a da Yaki da Cin hanci da Rashawa ta Jihar (PCACC).
Sakataren Labarai na Fadar Gwamnatin Kano, Abba Anwar ne ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.
Barista Mahmud, zai maye gurbin Muhuyi Magaji Rimin Gado, wanda a makon da ya gabata Majalisar Dokokin Jihar ta dakatar saboda ya ki amincewa da wani nadi da Gwamnati ta yi a Hukumar da yake jagoranta.
Gabanin wannan nadi, Barista Balarabe shi ne Darektan Gurfanar da Masu Laifi a Ma’aikatar Shari’a ta Jihar.
Aminiya ta ruwaito cewa, an dakatar da Barista Rimin Gado na tsawon wata guda saboda bai wa Kwamitin Yaki da Rashawa na Majalisar Dokokin Jihar damar gudanar da bincike kan zargin rashin da’ar da ake yi masa.
Rahotanni sun bayyana cewa, an dakatar da Rimin Gado ne saboda kin karbar sabon akantan da aka turo hukumarsa daga Ofishin Akanta Janar na Jihar Kano.
Dakatarwar, wacce ta fara aiki nan take, ta biyo bayan samun takardar korafi da Majalisar ta yi daga Ofishin Akanta Janar din ne a kan lamarin.
A makon jiya ne dai wasu rahotanni suka nuna cewa gwamnatin jihar ta Kano tana matsa wa majalisar lamba a kan ta sauke Barista Muhuyi saboda binciken da ya kaddamar a kan wasu dangin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Tsamin dangartaka tsakanin Ganduje da Muhuyi
Galibi dai ana zargin wannan takaddama ta kunno kai ne tsakanin Gwamna Ganduje da Barista, sakamakon wani bincike da ya kaddamar kan wasu kwangiloli da aka bai wa wasu iyalan Gwamnan.
Bayanai sun ce hukuncin da Rimin Gado ya yanke na binciken kwagiloli ciki har da na wata Cibiyar Yaki da Cutar Daji da aka bai wa ’yan uwan gwamnan ce ta janyo takaddamar.
Hakan ce ake ganin ta sa dangartaka ta yi tsami tsakanin bangarorin biyu, inda shi kuwa Muhuyi ya tabbatar da binciken da yake gudanarwa tare da cewa babu wata manufa daga gare sa kuma babu wanda zai raga wa muddin aiki ya biyo ta kansa.