Gwamnan jihar Kano Dokta Abdullahi Ganduje ya bayar da umarnin Salihu Tanko Yakasai ya koma bakin aiki bayan makonni biyu da dakatar da shi daga mukaminsa na mai ba gwamna shawara a kafafan watsa labarai.
Salihu Tanko Yakasai wanda ya fi shahara da inkiyar Dawisu musamman a dandalan sada zumunta, ya bayyana hakan da safiyar Alhamis a shafinsa na Twitter, inda ya mika godiyarsa ga jama’ar da suka taya sa farin cikin komawa bakin aiki.
- Hukumomi na tafka kuskure game da adabi —Rahma Abdul Majid
- Yadda ake bikin Maulidi a sassan Najeriya
“Ina mika godiya ga dukkan wadanda suka kira ni ko suka aikon min da sakonnin taya murnar mayar da ni bakin aiki na mai bada shawara kan kafafen yada labarai ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje, bayan makonni biyu da dakatar da ni.”
“Ina godiya gareku bisa goyon bayanku da addu’o’inku, a cewar Dawisu.
Makonni biyu da suka gabata ne Gwamna Ganduje ya dakatar da Salihu sakamakon wallafa wani sako da ya yi a shafinsa na Twitter yana sukar Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
A sakon da Dawisu ya wallafa, ya misalta Shugaban Kasar a matsayin mutum marar tausayi biyo bayan kurum din da Shugaban Kasar ya yi a kan kiraye-kirayen Matasa na neman rushe rundunar tsaro ta SARS, wanda faruwar hakan tasa Gwamnan ya dakatar da shi daga bakin aiki.
Kwanaki kadan bayan dakatarwar, Salihu ya bai wa Gwamnatin hakuri a shafukansa na sada zumunta da wasu shafukan jaridu bisa abin da ya wallafa a matsayinsa na makusanci ga Gwamnan kuma jami’in gwamnati.