Masu lura da harkokin siyasa na ganin Sanata Ibrahim Shekarau da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso manyan abokan hammaya ne da ba za su taba zama karkashin inuwa daya ba a siyasance.
A shekarar 2003, Shekarau (daga jam’iyyar ANPP a wancan lokaci) ya kayar da Gwamna Kwankwaso, mai neman wa’adin mulki na biyu a Jihar Kano.
Da Shekarau ya kammala wa’adinsa biyu na shekara takwas, ya nemi dan lelensa Salihu Sagir Takai ya gaje shi, amma ya kwashi kashinsa a hannun Kwankwaso, wanda ya mulki Jihar har zuwa 2011.
- Bayan shekaru 15 Bafarawa ya kai ziyara gidan Wamakko
- Zamfara: An cafke mahara a Fadar Sarkin Shinkafi
- Me ya sa El-Rufai bai yi ta’aziyyar Iyan Zazzau ba?
- Najeriya ba za ta taba rushewa ba —Lai Mohammed
Kwankwaso ya kara doke Shekarau a 2015, inda ‘zababben’ dan takararsa, mataimakinsa kuma Gwamnan Kano mai ci, Abdullahi Umar Ganduje ya kara kayar da Takai a zabe.
Gabanin haka, a 2014, Shekarau, wanda daya ne daga cikin iyayen jam’iyyar APC, ya sauya sheka zuwa PDP bayan shugabanninta sun mika ragamarta ga Gwamna Kwankwaso bayan ya dawo cikinta daga PDP.
Bayan shekara hudu Kwankwaso ya sake komawa PDP, inda nan ma shugabanninta suka mika masa shugabancinta a Jihar.
A wannan lokacin ma Shekarau ya sake ficewa daga jam’iyyar PDP ya koma APC din da Kwankwaso ya baro.
Hakan ta sa masu sharhi kan siyasar Kano ke ganin Shekarau da Kwankwaso ba za su zauna a jam’iyya daya ba.
A shekarar 2019, Shekarau ya maye gurbin Kwankwaso a kujerarsa ta dan Majalisar Dattawa mai wakiltar Kano ta Tsakiya, bayan ya kayar da dan takarar Kwankwaso da jam’iyyar PDP, Ali Madakin-Gini a zabe.
Da yawa sun yi hasashen cewa Ali Madakin-Gini sojan gonan ne kawai na Kwankwaso, wanda a lokacin tsohon Mataimakin Shugaban Kasa Atiku Abubakar ya kayar a zaben dan takarar Shugaban Kasar PDP.
Daga bisani, bayan rasuwar mahaifin Kwankwaso a ranar 25 ga watan Disamba, 2020, ziyarar ta’aziyyar da Shekarau ya kai masa, da wasu kalaman siyasa a baya-bayan nan sun sa masu sharhi a kan siyasar Kano ke ganin abokan hamayyar na neman su hada kai domin kwace ragamar siyasar Jihar Kano daga hannun Gwamna Ganduje a 2023.
‘Babu gaba’
An dade ba a ga-maciji tsakanin Kwankwaso da tsohon mataimakinsa, Ganduje, tun daga lokacin da Ganduje ya gaje shi a 2015.
Da yake amsa tambayar ’yan jarida a Kano ranar Lahadi, Shekarau ya ce babu wata gaba tsakaninsa da Ganduje ko Kwankwaso, kowannensu yana da kyakkyawar alaka da shi.
“Yanzu ba kwa ganin mu tare sosai ne saboda kun tura ni Abuja inda nake wakiltar mutanenmu.
“A takaice, dangantakar da ke tsakanina da Ganduje na da kyau matuka.
“Haka shi ma Kwankwaso muna da kyakkyawar alaka tsakanina da shi.
“Bambance-bambancenmu na siyasa ba su, kuma ba za su shafi alakar da ke tsakaninmu ba. Ban taba sau sheka daga wata jam’iyya zuwa wata saboda shi ba.
“Lokacin da nake APC, Kwankwaso ya shigo jam’iyyar, ni kuma na fita, amma da saboda da shi ba, sai saboda tsakanina da jam’iyyar.
“Abin da ya sake faruwa ke nan a lokacin da nake PDP, na fice daga jam’iyyar,” inji Shekarau.
Tuni dai aka fara shirye-shiryen zaben 2023, inda masu sharhi ke cewa akwai abin dubawa a kalaman na Shekarau, domin ruwa ba ya tsami a banza.
Yayin da wasu ke ganin cewa kalaman na Shekarau siyasa ce da aka saba gani, wasu na ganin ziyarar da ya kai wa Kwankwaso alama ce da ke nuna Ganduje na da jan aiki a gabansa na yin karon batta da tsoffin gwamnonin biyu a zaben 2023.