✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ganduje na yi mana katsalandan —Lauyoyin Abduljabbar

Muna kira da a tabbatar an yi wa wanda muke karewa adalci.

Lauyoyin malamin addinin musuluncin nan na Kano, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara sun zargi Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar da yin katsalandan a shari’ar wanda suke karewa.

Sun yi kira ga duk masu ruwa da tsaki da su sanya ido kan shari’ar don tabbatar an yi adalci.

‘Yan kungiyar asiri sun shiga hannu a Edo

Ba a kai wa Sarkin Kano hari ba —’Yan sanda

Lauyoyin karkashin jagorancin Barista Saleh M. Bakaro, sun yi wannan kiran ne a wani taron manema labarai a Kano ranar Lahadi.

A cewar su, “Abin da ya sa muka zanta da ku a yau shi ne bayyana rashin jin dadinmu kan rashin adalci da wani Babban Jami’in Gwamnatin Kano ke yi wa wanda muke karewa.

“Ya yi wasu kalamai masu tayar da hankali wanda muke ganin cewa son zuciya ne da kuma barazana ga shari’ar wanda muke karewa, Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara.”

A yayin ziyarar gaisuwar sallah babba da Ganduje ya kai wa Shugaban Darikar Kadiriyya, Sheikh Karibullah Nasiru Kabara a ranar Juma’a, ya ce gwamnatinsa za ta bi kadin shari’ar har zuwa karshenta.

Lauyoyin sun yi zargin cewa gwamnan ya kuma bayyana wanda suke karewa a matsayin ‘Maitatsine’ da kuma danganta shi da kungiyar Boko Haram.

A cewar Barista Bakaro, Gwamnan ya bayar da bayar da umarnin tsare wanda muke karewa a gidan gyaran hali wanda kuma bayar da umarnin ba huruminsa ba ne.

“Kuma wannan umarni kotu ce ya kamata a ce ta bayar a kan wanda muke karewa.

“A kan haka muke cewa kalaman gwamnan sun ci karo da shari’ar ma da ba a fara ta ba.

“Ya gama yanke hukuncin cewar wanda muke karewa ya yi kalaman batanci ga Manzon Allah (S.A.W), duk da cewar batun na gaban kotu, kuma wanda muke karewa ya musanta aikata hakan,” a cewarsa.

Lauyoyin sun kuma zargi Gwamna Ganduje da yin kalamai masu danganta Sheikh Abduljabbar da wasu kungiyoyin ‘yan ta’adda.

A ranar Juma’a 16 ga watan Yuli 2021, aka gurfanar da Abduljabbar a gaban kotun musulunci da ke zamanta a Kofar Kudu a birnin Kano, kan zargin yin kalaman batanci ga Manzon Allah (S.A.W).

Tuni kotun ta bayar da umarni ci gaba da tsare shi a gidan gyaran hali har sai ranar 28 ga watan Agustan 2021, inda za a ci gaba da sauraren shari’ar.