Rahotanni daga birnin Dabo sun yi nuni da cewa Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na Jihar Kano na fatan ganin mataimakinsa, Dokta Nasiru Yusuf Gawuna ya ci gajiyar kujerarsa a babban zaben 2023 da ke tafe.
Wakilinmu ya ruwaito cewa, hakan na zuwa ne a wani taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC wanda Gwamna Ganduje ya jagoranta.
- Tsohuwar matar shugaban APC ta fito takarar Gwamnan Nasarawa
- An sace magidanci a hanyar kai dansa jarabawar JAMB
Yayin taron wanda ya gudana a karshen makon nan, masu ruwa da tsaki sun kuma amince tsohon Kwamishinan Kananan Hukumomi da Harkokin Masarautu na Jihar Kano, Murtala Sule Garo ya zame wa Gawuna abokin takara.
Bayanai sun ce kusoshin jamiyyar ta APC ce suka shiga tsakanin wajen ganin Murtala Garo ya janye wa Gawuna takara.
Murtala Garo wanda babu shakka yana da ta cewa da kuma iko a tsarin jam’iyyar APC a matakin Kananan Hukumomi, shi ne dan takarar da uwargidan gwamnan, Hajiya Hafsat Ganduje ke marawa baya.
Ana iya tuna cewa dai, Ganduje shi ne ya yi wa tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso mataimaki a tsawon wa’adi biyu da suka shafe a gwamnati.
A wancan lokaci gabanin saukarasa, Kwankwaso ya ayyana Ganduje a matsayin wanda zai ci gajiyar kujerarsa, sai dai daga bisani dangarta ta yi tsami tsakaninsu jim kadan bayan kammala babban zabe na 2015.
Idan har ta kasance Gawuna ya lashe zaben gwamnan Kano a 2023, za a iya cewa a baya bayan nan al’adar mataimaki ya ci gajiyar kujerar ubangidansa ta samu gindin zama a siyasar Kano.