✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Ganduje da Dantata sun sasanta Dangote da BUA

Manyan dattawan Kano sun sasanta rikicin kamfanin sukari da BUA da Dangote

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya sasanta takun sadar da aka samu tsakanin Alhaji Aliko Dangote mai rukunin kamfanin Dangote da Alhaji Abdussamad Rabiu mai rukunin kamfanin BUA.

Ganduje tare da fittaccen mai kudi a Jihar, Alhaji Aminu Dantata da wasu dattawan jihar ne suka sasanta zaman doya da manjar da ke tsakanin manyan masu kudin biyu a kan kamfanoninsu na sukari.

Mai magana da yawun gwamnan, Abba Anwari, ya ce Masarautar Kano da malaman jihar sun shiga sasancin da aka yi, kan rikicin da ya kunno kai kan masana’antar sukari ta BUA.