✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ganduje bai ba ni miliyan 50 ba – Naziru M. Ahmad

Fitaccen mawaki, Nazir M. Ahmad wanda aka fi sani da ‘Sarkin Waka’ ya karyata batun jita-jitar da ake yadawa cewa Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar…

Fitaccen mawaki, Nazir M. Ahmad wanda aka fi sani da ‘Sarkin Waka’ ya karyata batun jita-jitar da ake yadawa cewa Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya ba shi tukwuicin Naira miliyan 50 sakamakon sabuwar wakar da ya yi masa.

Mawaki ya karyata batun jita-jitar ne cikin wata hira da ya yi da Aminiya, inda ya bayyana cewa jita-jitar ba ta da tushe ballantana makama.

“Wannan jita-jitar da ake yadawa ba gaskiya ba ce, ba ta da tushe ballantana makama. Na san dai mun gana da wakilan Ganduje, mun kuma kulla yarjejeniya da su, batun abin da muka tattauna kuwa ba zan fallasa shi ba.

“Amma batun da ake yadawa cewa an ba ni tukwuicin miliyan 50 ba gaskiya ba, ba zan fallasa me aka ba ni ba, amma idan bangaren gwamna Ganduje sun ga za su bayyana wannan kuma daga bangarensu ne, amma ni dai na san mun yi yarjejeniya cikin sirri,” inji shi.

Mawakin ya kuma gargadi mutane da su daina yada jita-jita domin babu wata riba da za su samu a cikin aikata hakan.

Da aka tambaye shi dalilin da ya sa yanzu ya mayar da hankali kan wakokin siyasa, maimakon ci gaba da yin wakokinsa ga masu sarauta ko attajirai ba, sai ya ce bai kamata mawaki ya raja’a a kan salon waka daya ba.

“A matsayin mutum na mawaki, bai kamata ya raja’a a kan salon waka daya ba, kada ya tsaya kikam a kan salon waka daya kamar bishiyar Iroko, ya kamata a san mawaki da sauyawa zuwan yin kowane irin salo. A yanzu da aka tunkarin zaben 2019 zan mayar da hankalina ga wakokin siyasa, kuma na fara da Gwamna ganduje ke nan, amma zan rika yin wakoki ba tare da cin mutunci ko hantara ba,” inji shi.