✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gwamna Akeredolu na Ondo ya kamu da COVID-19

Gwamna Rotimi Akeredolu na Jihar Ondo da ke Kudu-maso-Yammacin Najeriya ya kamu da cutar COVID-19. Gwamna Akeredolu a cikin wani bidiyo, ya ce sakamakon gwajin…

Gwamna Rotimi Akeredolu na Jihar Ondo da ke Kudu-maso-Yammacin Najeriya ya kamu da cutar COVID-19.

Gwamna Akeredolu a cikin wani bidiyo, ya ce sakamakon gwajin cutar da aka yi masa ya nuna cewa yana dauke da kwayar cutar COVID-19, kuma zai fara killace kansa, domin likitoci su kula da lafiyarsa.

“Sakamon ya fito yau Talata 30 ga watan Yuni, 2020 kuma na kamu da cutar.

“Likitocina sun yanke shawarar cewa in fara karbar magani, in kuma killace kai na”, inji shi.

Gwamnan wanda ya ce alamar cuatar tasa ta fara ne daga zazzabin malaria ya shawarci masu jin alamar malariya a jihar da su je a yi musu gwaji.

Ya kuma bukaci jami’ai da mukarraban gwamnatinsa da su ci gaba da gudanar da ayyuka yadda suka saba, yana mai cewa shi ma zai ci gaba da gudanar da aikinsa daga killace.