✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gambo Mohammed ya koma Filato United

dan kwallon gaba a kulob din Kano Pillars Gambo Mohammed ya sanu nasarar canza sheka zuwa kulob din Filato United da ke Jos. Kamar yadda…

dan kwallon gaba a kulob din Kano Pillars Gambo Mohammed ya sanu nasarar canza sheka zuwa kulob din Filato United da ke Jos.

Kamar yadda jaridar Completesport mai buga labarin wasanni ta kalato, an nuna dan kwallon ya sanya hannu ne a kwantagarin shekaru biyu da Filato United.

Sai dai kafin nan, an yi ta rade-radin dan kwallon zai koma kulob din Ribers United ne amma sai aka ji ya sanya wa Filato United hannu da hakan ya kawo karshen rade-radin.

Gambo Mohammed dan shekara 29, tun a shekarar 2006 yake yi wa kulob din Pillars kwallo inda ya samu nasarar lashe kofunan gasar firimiyar Najeriya har sau 3 da Pillars.

Duk da ba a ambaci yawan kudin da Filato United ta sayi dan kwallon ba rahotanni sun ce Pillars ta nemi zunzurutun Naira miliyan 15 ne ga duk kulob din da ke bukatarsa.

Filato United ce ta lashe gasar firimiyar Najeriya a bana, kuma za ta buga Gasar Cin Kofin Zakarun Kulob na Afirka (Champions League) al’amarin da ya sa suke zawarcin zaratan ’yan kwallo kafin a fara gasar.