✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

Galadiman Bauchi ya yi gargadi a kan illar sare itatuwa

Galadiman Bauchi Hakimin Zungur, Alhaji Sa’idu Ibrahim Jahun, ya yi kira ga al’ummar masarautarsa su guji sare itatuwa domin guje wa kwararowar hamada. Alhaji Sa’idu…

Galadiman Bauchi Hakimin Zungur, Alhaji Sa’idu Ibrahim Jahun, ya yi kira ga al’ummar masarautarsa su guji sare itatuwa domin guje wa kwararowar hamada.

Alhaji Sa’idu Jahun ya yi wannan kira ne a lokacin da yake zantawa da Aminiya a fadarsa.

Ya ce, “Maganar sare itatuwa na damun hakimai, musamman ni kaina saboda masu sare itatuwan ba su san illar haka ba.”

“A gaskiya illarsa tana da yawa. Idan ana yawan sare itatuwa ko ba muga illarsa yanzu ba, za mu gani a gaba don muhallinmu zai gurbace baki daya,” inji shi.

Ya ce “A da idan za a sare itace sai an ba da dama kuma da gatari ake yi. Wanda zai sare itace da gatari kwana nawa zai yi kafin ya kada bishiya?

Yanzu kuwa sai a ce an ba ka lasisi, kai kuma sai ka nemo inji kawai ka je ka kama sare itatuwa. Wannan ba daidai ba ne.”

Galadiman ya ce ya kamata karamar hukuma ta farfado da ayyukan sarakunan daji, a ba su damar hana sare itatuwa don kare kwararowar hamada.