✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Gabon: Sojoji sun ba Bongo damar fita waje neman magani

Sojoji da suka yi juyin mulki a Gabon, sun bai wa hambarerren shugaban kasar Ali Bongo da ke tsare damar  yin balaguro zuwa kasashen waje…

Sojoji da suka yi juyin mulki a Gabon, sun bai wa hambarerren shugaban kasar Ali Bongo da ke tsare damar  yin balaguro zuwa kasashen waje domin duba lafiyarsa.

Jagoran juyin mulkin Janar Brice Oligui Nguema wanda ya hambarar da Ali Bongo ya kuma sha rantsuwar kama aiki a matsayin shugaban rikon kwarya ya ce mista Bongo na da cikakken ‘yanci, kamara yadda ya bayyana cikin sanarwa da aka karanta a gidan talabijin na kasar.

“Yana da ‘yancin walwala… ciki harda tafiya kasashen waje idan ya ga dama,” in ji Janar Brice Oligui Nguema.

Bongo, wanda ya shafe shekaru 14 a kan karagar mulki, ya kasance a tsare tun bayan juyin mulkin da sojoji suka yi a ranar 30 ga watan Agusta, kasa da sa’a guda bayan da hukumar zaben kasar ta sanar da nasara sa ta yin tazarce, wanda jam’iyyun adawa suka bayyana a matsayin an tafka magudi.

“Idan aka yi la’akari da yanayin lafiyarsa, tsohon shugaban kasar Ali Bongo Ondimba yana da ‘yancin yin tafiya, zai iya tafiya kasashen waje idan yana bukatar duba lafiyarsa,” in ji Kanar Ulrich Manfoumbi Manfoumbi, yayin karanta wata sanarwa da Oligui ya sanya wa hannu.

Rashin lafiyar Bongo

Bongo na fama da matsananciyar ciwo na shanyewar jiki tun a watan Oktoban 2018 wanda hakan ya sa ya samu nakasu a jiki, wanda ya haifar masa da cikas musamman wajen motsa kafarsa da hannunsa ta dama.