✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ga shugaban karamar Hukumar Sabon-birni

Kira ga Shugaban karamar Hukumar Sabon-birni. Assalamu alaikum Aminiya ana cewa Idris Gobir ya yi aiki, ya yi famfuna da makarantu, amma mu ba aiki…

Kira ga Shugaban karamar Hukumar Sabon-birni. Assalamu alaikum Aminiya ana cewa Idris Gobir ya yi aiki, ya yi famfuna da makarantu, amma mu ba aiki ya yi mana ba, sai dai ya kwace mana gona. Ka ji tsoron Allah ka biya iyayenmu diyyar gonakinmu. Daga Bala G. Gobir 08061167405.

Sakonnin waya

Jonathan ga ASUU
Salam Aminiya ku gaya wa majalisun kasa su tilasta wa Jonathan ya biya bukatun ASUU, domin mu talakawa mu koma makaranta. Daga Ibrahim UMYUK, Katsina 08186322112.

Addu’a ga Mursi
Al’ummar Musulmi ku himmatu da addu’a, Allah Ya kawo wa Shugaban MAsar Muhamamd Mursi dauki. Daga Ali Fancy garko A. Kano  08171748500.

Sarakuna ga Jami’a
Salam. Wai sarakunan Arewa ga Foliyo (rigakafin Shan inna) kawai suke magana, ban da  ilimin Jami’a. Daga Ibrahim Katsina

A kawo dauki ga ASUU
Editan Aminiya shawara game da yajin aikin malaman jami’a ’yan majalisun wakilai da na dattawa da su kawo karshen yajin aiki. Daga Yusuf A. Yusuf Gama Kano 08059866798.

Jinjina ga Aminiya
Jinjinar girmamawa  Ina jinjina ga wannan jarida ta Aminiya. Gaskiya tana da dadin karatu. Daga Tajuddeen Sa’idu Mahuta 08073216330.

Jinjina ga Kwankwaso
Jinjina ta musamman ga Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso. Assalamu alaikum don Allah Aminiya ki mika min sakona ga Dokta Rabi’u Musa Kwankwaso, Gwamnan Jihar Kano.  Muna tare da kai. Daga Nura Buhari Bodinga Lalas 07033155737.

Ya za a raba Najeriya?
Yaya za a raba Najaeriya, sannan kudin da ke wajen Najeriya da ba shi duk a raba. Daga sai batun rabuwa. Daga Yusuf Sani Sakkwato 0806832246.

Don talakawa APC
Sakkwatawa mu hada hannu karfi da karfe, mu ceto jiharmu da kasarmu baki daya mu kafe, mu dage mu yi jam’iyyar APC, don talaka da talakawa. Mu ceto arewa da kasarmu baki daya; mu bi Garkuwan Sakkwato, wato Attahiru Bafarawa a shekarar 2015, muna bayanka Bafarawa. Daga Musty Sakkwato 08034068363.

Ga malaman jami’a
Zuwa ga Edita, don Allah ka isar min da sakona ga malaman jami’a. Ku tuna fa abin dakuka shuka ne kuke girba. Da ku aka hada kai aka kafa mana wannan gwamnatin, don ku ne kuka uba zaben da ya jawo tashin hankali a Najeriya. Daga Adamu Mai Farare 08065871836.

Fadakarwa ga Shema
Gkaskiya mu ji tsoron Allah don gaskiya za mu mutu, kuma akwai hisabi. Yanzu babbar asibitin Katsina a ce wai har safar hannu, sai amrar lafiya ya saya. To Allah dai na ganinka. Daga Hamza Darma 07036362698.

Ga Sule Lamido
Assalamu alaikum. Haba Gwamna Lamido, ya haka kai da muke ganin kai ne jarumi, amma sai zama matsoraci. Daga Usman Bala G. Ningi 08151569164.

PDP kin kusa zama zindikin itace, ba reshe, ba ganye, ballantana a sha inuwa. Daga Ibrahim AB Balarabe Zariya 08023429001.

Ga Aminiya
Aminiya don Allah ku rika turo min labarai. Daga Injiniya TGZ, kamar Hukumar Sakkwato. 08037241390.

Ga Gwamna Shema
Salam Edita don Allah ka ba ni dama in yi kira ga Gwamnan Jihar Katsina da ta gudanar da zaben kananan hukumomi. Domin rashin haka yasa mutane ke fama da talauci, don yawanci jam’a ba su san inda ake kira rabon da ake karbewa na gwamantin tarayya ba. Daga Rabi’u Baba Lawal Funtuwa. 08153171016.

Hassada mugun ciwo
Salam yau mun samu kanmu a cikin wani zamani da cutar hassada tayi yawa a tsakanin jam’a a cikin mutane akwai wadanda hassada ta riga ta yi musu kanta a zukatansu. A ji tsoron Allah a daina. Daga Nasiru Albani Bauchi 08167155483.

Jam’iyyar APC ce mafita
Al’ummar kasar nan duba yadda mutane ke komawa jam’iyyar tagomashi, sdannan kuma talakawan Najeriya sun karbeta. Tafiya ka’in da na’in, fatanmu Allah Ya sa hakan ya zame wa kasarmu alheri. Daga Mubarak Yunus Ya’akub Tudun Murtala Nassarawa, Kano. 07061956150.

Abubakar Ladan
Alhaji Abubakar Ladan da kashin yadawa ba ne. Editar jaridar Aminiya jarida mai farin jinni da kwarjini. Salamun Alaikum. A yau na so ne na yi tsokaci, akan, irin baiwa da hikimomi da Allah ya bai wa Abubakar Ladan Zariya da kowa ya amfana a kasar nan da Afirka da ma kasashen duniya. Kowa ya sha romon baiwar Abubakar ladan. Daga Abubakar Sifawa Rima Rediyo Sakwato 08065717934.

Sasantawa ce mafita
Sasantawa da Masu tada zaune zaune tsaye ne mafita ba wai sanyama talakkawa Dokar ta baci ba. Daga AbdulMalik sa’idu Mai Biredi Tashar Bagu, Gusau. 08069807496.

Auren Zawarawan Sakkwato
Hakika ko shakka babu matakin matakin da Gwamnatin Jihar sakkwato ta dauka na aurar da Gwauraye 250 duk bayan wata ukku ya dace. Sai dai hanzari ba gudu ba, a kauce wa sanya siyasa acikin wannan aiki na alheri. Da fatan Allah ya kyauta. Daga: Hassan Muhammad Binanchi,Daga Unguwar Magajin Garin Sakkwato

Ga makiyan Najeriya
Makiyan Najeriya, da kuna so, ko ba ku so, sai kasar nan t ayi kyau a karkashin  inuwar Jam’iyyar APC, insha Allah. Daga 07068223015.

Ga ’yan mata
Gareku ’yan mata ku kasance masu shiga ta mutunci, domin hakan zai kara muku kima da daraja. Kuma ta haka ne za ku samu mazaje nagari. Daga Abdulkadir S. Harbo 08145200380.