✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ga barawo ga mai kaya

Wani mai tura baro ne sai wani barawo ya sato buhun wake ya ba shi dako, to da barawon ya ga cewa mai kaya ya…

Wani mai tura baro ne sai wani barawo ya sato buhun wake ya ba shi dako, to da barawon ya ga cewa mai kaya ya gano shi, sai ya gudu ya bar dan baro da buhun wake aka kama shi, ya ce shi fa dako aka ba shi. Ina wanda ya ba shi dako? Babu shi babu alamarsa, ya gudu. Da aka je caji ofis, na fara yi masa tambayoyi, sai ya ce: “Dandan dandan dandan! Ga barawo, ga mai kaya.” Sannan sai ya dubi dan sandan da ke yi masa tambayoyi ya ce: “Yallabai me kake jira ga ka da bindiga ka harbe ni kawai.”
Daga Salihu Makera, 07086866165.