Shugabannin kasashe masu karfin tattalin arziki (G20) sun bukaci sauran kasashe su tabbatar an samar da wadataccen rigakafin cutar coronavirus a ko’ina a duniya.
Da yake kiran, Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, ya ja hankalin sauran shugabannin kasashe da su bayar da tasu gudunmawar domin ganin rigakafin ya wadata a fadin duniya.
- Saudiyya na jagorantar taron G20 kan inganta rayuwa bayan COVID-19
- An dakatar da Kwamandan Hisbah kan karkatar da kayan tallafi
- Mahara sun kashe shugaban dalibai a Kaduna
Ita ma Shugabar Jamus Angela Merkel, ta kirayi sauran shugabannin da su sanya wadattun kudade wajen samar da rigakafin cutar domin ya samu a ko’ina.
Sai dai Shugaba Trump na Amurka bai halarci taron na yaki da annobar coronavirus da inganta rayuwar jama’a bayan shudewarta ba.
An fara taron na G20 na kwana biyu ne a kasar Saudiyya ranar Asabar 21 ga watan Nuwamba, bisa jagorancin mai masaukin baki, Sarki Salaman bin Abdulazeez na Saudiyya.